NAFDAC ta kama kwayoyin tramadon da kudin sa ya kai N193bn a shekara 1

NAFDAC ta kama kwayoyin tramadon da kudin sa ya kai N193bn a shekara 1

Farfesa Mojisola Adeyeye, Darakta Janar na hukumar kula da kayayyakin abinci da magunguna (NAFDAC) ta ce hukumar ta kama kwayoyin Tramadol sama da guda biliyan shida wanda farashin su ya kai naira biliyan 193.

Adeyeye ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, inda ta gabatar da rahoton ta na shekara daya tun daga lokacin da ta fara aiki aiki a matsayin darakta janar na hukumar.

Ta bayyana cewa a lokacin binciken, hukumar ta kama kwalaye 321,146 na magungunan da ba’a yi wa rijista ba wanda farashin su ya kai miliyoyin naira.

NAFDAC ta kama kwayoyin tramadon da kudin sa ya kai N193bn a shekara 1

NAFDAC ta kama kwayoyin tramadon da kudin sa ya kai N193bn a shekara 1
Source: Depositphotos

Hukumar ta sanya an hukunta daga cikin masu raba tramadol yayinda aka gurfanar da sauran uku a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Lagas.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: Buratai ya bukaci dakarun soji da su dauki yanayi mai tsauri

Ta kuma bayyana cewa kotu ta yi umurnin lalata kayyakin da aka kwace, tare da bayanin cewa hukumar ta kammala duk wani shiri don lalata kwataina sama da 30 na tramadol da sauran kayayyakin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel