INEC na barazanar cire wasu 'yan Takarar shugaban kasa, sun saba dokar zabe

INEC na barazanar cire wasu 'yan Takarar shugaban kasa, sun saba dokar zabe

- Shugaban INEC yace zasu cire sunayen yan takarar jam'iyyun da suka ki bin dokokinsu

- Wasu jam'iyyun sun tsayar da yan takarar shugabancin kasa masu shekaru kasa da 35

- INEC bazata lamunci yiwa dokokin zabe karan tsaye ba

INEC na barazanar cire wasu 'yan Takarar shugaban kasa, sun saba dokar zabe

INEC na barazanar cire wasu 'yan Takarar shugaban kasa, sun saba dokar zabe
Source: UGC

Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a ranar Alhamis 29 ga watan Nuwamba, ya zargi wasu jam'iyyun siyasa da laifin kawo sunayen wadanda shekarun su bai kai ba don tsayawa takarar shugabancin kasa.

Yakubu ya sanar da manema labarai yanda suka gano sunayen wadanda basu kai shekaru 35 ba a matsayin yan takarar shugabancin kasa da mataimakan su.

"Mun jawo hankulan jam'iyyun da abin ya shafa akan yiwa kundin tsarin mulkin kasa karan tsaye."

DUBA WANNAN: Laifi da hukunci: Shin mai aiki da ya kashe ogansa ya mutu ne ko yana raye?

"Bamuyi ba kuma bazamu taba lamuntar yiwa doka karan tsaye ba. A yanzu da aka gama gyara ko janye sunayen yan takarar, jimillar jam'iyyun siyasa 73 ne suka kawo sunayen yan takarar su na shugabancin kasa."

"A majalisar dattawa, yan takara 1,848 ne suke neman kujerun sanatoci 109. Sai majalisar wakilai akwai yan takara 4,635 dake neman kujeru 360." inji Yakubu

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel