Boko Haram: Buratai ya bukaci dakarun soji da su dauki yanayi mai tsauri

Boko Haram: Buratai ya bukaci dakarun soji da su dauki yanayi mai tsauri

Shugaban hafsan sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai ya bukaci kwamandojin da ke filin daga da su dauki matakin da ya kamata wajen hukunta yan ta’addan Boko Haram da hukunci mai tsauri.

Buratai ya bukaci hakan ne a ranar Juma’a, 30 ga watan Nuwamba a Maiduguri a karshen taron ranar sojoji.

Ya bayyana cewa akwai bukatar yin hakan do tsorata yan ta’adda.

Buratai ya gargadi dakarun sojin da kada su bari harin da yan ta’addan suka yi a kwanan nan musamman a Metele, inda yan ta’addan suka far ma sojojin Bataliya 157, suka kashe 23 tare da raunata wasu.

Boko Haram: Buratai ya bukaci dakarun soji da su dauki yanayi mai tsauri

Boko Haram: Buratai ya bukaci dakarun soji da su dauki yanayi mai tsauri
Source: Depositphotos

A cewarsa, lamarin habbaka kayayyakin dabarun yaki zai basu damar cimma nasara wajen kare sansanin su da filin daga.

KU KARANTA KUMA: Dino Melaye ne mai magana da yawun kwamitin takarar Atiku

Ya nuna farin ciki kan cewa an cimma manufar taron na kwanaki uku amma ya bukaci kwamandojin das u tabbatar da sun dauki matakan da suka dace.

Shugaban sojin ya kuma yi amfani da damar wajen bayyana cewa rundunar ba zata sanya kanta a harkar siyasa ba a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel