Buratai ya bada odan bincike kan sansanin horar da yan bindigan da aka gano a jihar Ribas

Buratai ya bada odan bincike kan sansanin horar da yan bindigan da aka gano a jihar Ribas

Babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Yusufu Buratai, ya bada umurnin gudanar da bincike mai zurfi cikin sansanin horar da yan bindigan da aka gano a karamar hukumar Tai a jihar Ribas.

Legit.ng Hausa ta samu wannan labari ne daga shafin sada ra’ayi da zumuntar hukumar na Tuwita inda yace:

“Babban hafsan sojin Najeriya, Laftanan Janar Tukur Yusufu Buratai ya bada umurnin gudanar da bincike mai zurfi kan sansanin horar da yan bindigan da rundunar 6 Division suka gano a sansanin masu bautar kasa dake Nonwa Gbam, karamar hukumar Tai, jihar Ribas.”

Buratai ya bada odan bincike kan sansanin horar da yan bindigan da aka gano a jihar Ribas

Buratai ya bada odan bincike kan sansanin horar da yan bindigan da aka gano a jihar Ribas
Source: Depositphotos

KU KARANTA; Hukumar yan sanda ta damke yan baranda

Mun kawo muku rahoton cewa hukumar Sojin Najeriya ta ce jami'anta sun gano wani haramyaccen sansanin bayar da horo na fada da bindiga a Nonwa Gbam (sansanin horas da 'yan yiwa kasa hidima) a karamar hukumar Tai da ke jihar Rivers.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kungiyar dattawan Ogoni sun zargi Ma'aikatar Muhalli na Kasa da kawo dakarun sojoji zuwa garuruwan Ogoni domin samar da tsaro yayin da ake aikin tsaftace garuruwan da danyen man fetur ya gurbata.

Mataimakin Direktan yada labarai na sojin, Aminu Iliyasu ya ce dakarun sojojin sun gano sansanin bayar da horon ne yayin da suke kewaya garin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel