Da dumi dumi: Jam'iyyar APGA ta dare gida biyu, sabon rikici ya mamaye jam'iyyar

Da dumi dumi: Jam'iyyar APGA ta dare gida biyu, sabon rikici ya mamaye jam'iyyar

- Rikicin ya mamaye jam'iyyar APGA tun bayan da jam'iyyar ta yi mubayi'a ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, karshe a ranar Juma'a, jam'iyyar ta rabe gida biyu

- Sabuwar jam'iyyar mai suna Authentic All Progressives Grand Alliance (AAPGA), na a karkashin shugabancin Jerry Obasi, yayin da A.D. Musa ya kasance sakatarenta

- Shuwagabannin sabuwar jam'iyyar ta AAPGA, sun yi Allah wadai da yadda gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, ya yi mubayi'a ga takarar shugaban kasa Buhari

Rikicin da ya mamaye jam'iyyar APGA tun bayan da jam'iyyar ta yi mubayi'a ga dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari ya dauki sabon salo, inda a ranar Juma'a, aka samu bulluwar wata sabuwar jam'iyyar, wacce ta balle daga uwar jam'iyyar.

Sabuwar jam'iyyar mai suna Authentic All Progressives Grand Alliance (AAPGA), na a karkashin shugabancin Jerry Obasi, yayin da A.D. Musa ya kasance sakatarenta.

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Juma'a, sabon shugaban tsagin jam'iyyar, ya ce muna kalubalantar APGA da nuna son kai da tauye hakki a siyasance dangane da makomarta a harkokin zaben kasar.

KARANTA WANNAN: Batun wai Buhari ya tsige Sifeta Janar wani wasan yara ne - Rundunar 'yan sanda ta caccaki PDP

Da dumi dumi: Jam'iyyar APGA ta dare gida biyu, sabon rikici ya mamaye jam'iyyar

Da dumi dumi: Jam'iyyar APGA ta dare gida biyu, sabon rikici ya mamaye jam'iyyar
Source: Depositphotos

Shuwagabannin sabuwar jam'iyyar ta AAPGA, sun yi Allah wadai da yadda gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, wanda shine shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar APGA ya yi mubayi'a ga takarar shugaban kasa Buhari a madadin jam'iyyar.

"Don haka muna kira ga Gwamna Willie Obiano na jihar Anambra da ya yi murabus daga shugabancin kwamitin amintattu kuma jagoran APGA, duba da rashin ladabi da da'ar da ya nuna na fitowa fili tare da bayyanawa jama'a cewa APGA ta amince shugaban kasa Buhari ya zama dan takararta ba tare da tuntubar kwamitin zartaswa na kasa ba," a cewar shugaban sabuwar jam'iyyar ta AAPGA.

A wani taron kaddamar da wani littafi a Abuja, Obiano ya jagoranci wani sashe na shuwagabannin jam'iyyar wajen bayyana mubayi'arsu ga Buhari da kuma rike shi a matsayin dan takararsu, ba tare da la'akari da cewa APGA ta tsayar da Janar John Gbor a matsayin dan takarar shugaban kasar ba.

Sai dai ta sanar da kafa wasu kwamitoci guda ukku da zasu warware wannan rikici da ya mamaye jam'iyyar. Kwamitocin sun hada da kwamitin tantancewa kan sha'anin siyasa, wanda zai tantance tare da nazarin harkokin siyasar jam'iyyar musamman don fuskantar zaben 2019.

Sauran kwamitocin sun hada da kwamitin tuntuba, wanda zai gana da duk wasu mambobin jam'iyyar da suke ganin ba'ayi masu adalciba a zabukan fitar da gwani da sauran sha'anoni na jam'iyyar; da kuma kwamitin sauraron korafe korafe, wanda zai saurari korafe korafe daga mambobin jam'iyyar don warwaresu tare da wanzar da hadin kai a jam'iyyar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel