Abin kunya: An kama wasu sun saci wayar salula a masallaci

Abin kunya: An kama wasu sun saci wayar salula a masallaci

'Yan sanda sunyi gurfanar da wasu mutane biyu Tijjani Rasheed da Tosin Oluwafemi da ake zargi da satan wayon salula a masallaci a gaban kotun Majistare da ke Ile-Ife.

Dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Emmanuel Abdullahi ya shaidawa kotu cewa wadanda ake zargin su aikata laifin ne a ranar 28 ga watan Nuwamban 2018 misalin karfe 6 na safiya a Odi Iredumi Oke-Atan a Ile-Ife.

Abdullahi ya ce mutane biyun da ake zargi sun hada baki ne wajen aikata laifin.

Abin kunya: An kama wani ya saci wayar salula a masallaci

Abin kunya: An kama wani ya saci wayar salula a masallaci
Source: Twitter

Ya yi ikirarin cewa wadanda ake zargin sun shiga masallacin da ke Odi Iredumi Oke-Atan, Ile Ife sannan suka sace Itel 2016 mallakar wani Gani Olihu wadda kudinsa ya kai N38,000 a yayin da ya ke sallah a masallaci.

DUBA WANNAN: Bidiyon Ganduje: 'Yan majalisun tarayyar APC na jihar Kano sun fadi ra'ayoyinsu

Mai shigar da karar ya ce laifin da ake zarginsu da aikatawa ya ci karo na sashi na 383, 390 (9), 411 da 516 na dokar masu laifi na jihar Osun, 2002.

Sai dai wadanda ake zargin sun ce basu aikata laifin sata da hadin bakin da ake zarginsu da shi ba.

Lauya mai kare wadanda ake tuhuma, Ben Adirieje ya roki kotu ta bayar da belinsu tare da yin alkawarin cewa ba za su gudu ba kuma zai samo mutane da za su karbi belin na su.

Alkalin kotun, Adejumoke Ademola-Olowolagba ta amsa rokon lauyan mai kare masu laifin inda ya bayar da belinsu a kan kudi N100,000 kowannensu tare da gabatar da mutane biyu da za su tsaya musu.

Ademola-Olowolagba ta dage cigaba da sauraon shari'r zuwa ranar 21 ga watan Disamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel