Da duminsa: Daga dawowa daga Chadi, Shugaba Buhari zai tafi kasar Poland gobe Asabar

Da duminsa: Daga dawowa daga Chadi, Shugaba Buhari zai tafi kasar Poland gobe Asabar

Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja domin zuwa birnin Katowice, kasar Poland, rana Asabar domin halartan taron gangamin duniya kan canjin yanayi karo na 24 na majalisar dinkin duniya wato UNFCCC.

Wannan taro na shugabannin duniya zai gudana ne daga rana 2 ga watan Disamba zuwa 5.

Game da cewar wadanda suka shirya taro, ana kyautata zaton kammala magana kan aiwatar da shawarwarin da ke cikin yarjejeniyar canjin yanayi da akayi a kasar Faransa wato "Yarjejeniyar Paris".

A taron, mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaba Buhari zai gabatar da jawabi kan irin namijin kokarin da gwamnatin Najeriya keyi wajen dakile canjin yanayi ta hanar aiwatar da ayyukan da ta shirya.

Bayan hakan, Buhari zai gana da yan Najeriya mazauna kasar Poland. Kana zai gana da shugaban kasar Poland, Andrzej Duda da firam ministan kasar Mateusz Morawiecki.

Daga cikin wadanda zasu takawa Buhari baya sune gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuwanyi; gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello; da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello.

Sauran sune ministan harkokin wajen Najeriya, Geofrey Onyeama; ministan ayyukan ruwa, Suleiman Adamu, da karamin ministan yanayi, Ibrahim Jibrin.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel