Kotu ta soke afuwar da Tambuwal ya yiwa wasu da ake zargi da satar N15bn

Kotu ta soke afuwar da Tambuwal ya yiwa wasu da ake zargi da satar N15bn

- Kotun daukaka kara da ke zamanta a Sokoto soke afuwar da Gwamna Tambuwal ya yiwa wasu da ake zargi da karkatar da biliyan 15m

- Kotun daukaka karar ta ce afuwar ba sabawa ka'ida saboda kotu ba ta tabbatar da laifukan ba kuma ba a yanke musu hukunci ba

- Kotun ta umurci wasu daga cikin wadanda ake zargin su garzaya zuwa kotu domin fuskantar shari'ar da su keyi da EFCC

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Sokoto ta soke afuwar da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yiwa wasu mutane biyu hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati EFCC ta gurfanar a kotu bisa zarginsu da sace Naira Biliyan 15 mallakar gwamnatin jihar Sokoto.

Legit.ng ta gano cewa alkalin kotun biyar karkashin jagorancin mai shari'a Hannatu Sankey ne suka yanke wannan hukuncin a ranar Alhamis 29 ga watan Nuwamban shekarar 2018.

Kotu ta soke afuwar da Tambuwal ya yiwa wasu da ake zargi da sace N15bn da asusun jihar Sokoto

Kotu ta soke afuwar da Tambuwal ya yiwa wasu da ake zargi da sace N15bn da asusun jihar Sokoto
Source: Twitter

Vanguard ta ruwaito cewa gwamnan ya yi afuwa ga tsohon sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi da Isa Sadiq Achida duk da cewa basu gurfana gaban kotu ba sakamakon karar da EFCC ta shigar a kansu.

DUBA WANNAN: Bidiyon Ganduje: 'Yan majalisun tarayyar APC na jihar Kano sun fadi ra'ayoyinsu

An ruwaito cewa gwamnan ya yi amfani da karfin ikon da doka ta bashi ne wajen yi musu afuwar.

A yayin yanke hukuncin, kotun ta ce ba dai-dai bane gwamnan ya yiwa wani afuwa alhalin ba a tabbatar da laifi akansa ba domin har yanzu shari'ar na gaban kuliya.

Mai shari'a Sankey da mai shari'a Ndukwe-Anyawu sun ce a halin yanzu mutane biyu da aka yiwa afuwar ba masu laifi bane saboda kotun ba ta tabbatar da laifin da ake zarginsu da aikatawa ba saboda haka batun afuwa bai taso ba.

Daga nan, kotun ta umurci wadanda ake tuhumar su gurfana a gaban kotu domin kare kansu daga zargin satar da ake musu.

Ana tuhumarsu ne tare da tsohon gwamnan jihar Sokotom Attahiru Dalhatu Bafarawa kan sace zunzurutun kudi sama da Naira Biliyan 15. Sauran mutanen da ake tuhuma sun hada da Alhaji Tukur Alkali, Bello Isah da Alhaji Halilu Modachi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel