Batun wai Buhari ya tsige Sifeta Janar wani wasan yara ne - Rundunar 'yan sanda ta caccaki PDP

Batun wai Buhari ya tsige Sifeta Janar wani wasan yara ne - Rundunar 'yan sanda ta caccaki PDP

- Rundunar 'yan sanda ta maidawa jam'iyyar APC martani kan bukatar da ta gabatarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari, na tsige Sifeta Janar kafin babban zabe na 2019

- Rundunar ta bayyana wannan kira da PDP ta yi na Sifeta Janar ya yi murabus daga kujerarsa da kansa a masatin wani wasan yara da ya kamata ayiwa dariya

- A taron PDP a Abuja, Atiku Abubakar, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsige Sifeta Janar na rundunar 'yan sandan kafin zaben 2019

Rundunar 'yan sanda ta maidawa jam'iyyar APC martani kan bukatar da ta gabatarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari, na tsige Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda (IGP) kafin babban zabe na 2019.

A ranan Alhamis, jami'in hulda da jama'a na rundunar, Mr Jimoh Moshood, ya yi watsi da wannan zarge-zargen da jam'iyyar PDP ta gabatar akan Sifeta Janar din, na cewar yana da sauyin sauya akala musamman idan akazo batun zabe.

Ya kuma bayyana wannan kira da PDP ta yi na Sifeta Janar din ya rubuta takardar murabus daga kujerarsa da kansa a masatin wani wasan yara da ya kamata ayiwa dariya.

KARANTA WANNAN: Boko Haram: Har yanzu muna fuskantar hare hare - Shehun Borno ya shaidawa Buhari

Batun wai Buhari ya tsige Sifeta Janar wani wasan yara ne - Rundunar 'yan sanda ta caccaki PDP

Batun wai Buhari ya tsige Sifeta Janar wani wasan yara ne - Rundunar 'yan sanda ta caccaki PDP
Source: Depositphotos

A fuskantar babban zabe na 2019, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da kasancewa maras nuna bangaranci ko shiga harkokin siyasa, kuma ba za ta fifita wata jam'iyya akan wata ba.

Don haka, ya kalubalanci jam'iyyar PDP da ta sanar da jama'a ko ta rubuta rahoto kan lokutan da rundunar 'yan sanda ta taba sauya akalarta, tare da jaddada cewa rundunar 'yan sanda ta mayar da hankali ne kawai wajen tabbatar da cewa an gudanar da zabukan 2019 lami lafiya.

Wannan jawabin nasa, martani ne ga jawabin shugaban jam'iyyar PDP na kasa Mr Uche Secondus, wanda ya zargi Sifeta Janar da hada baki da jam'iyya mai mulki wajen cafke abokan hamayya da tsare su.

Secondus wanda ya yi jawabi a taron kwamitin zartaswa na jam'iyyar na kasa da ya gudana a Abuja, ya bukaci shugaban hukumar INEC na kasa Farfesa Mahmood Yakubu, shima da ya yi murabus daga wannan mukami nasa.

A taron, shima dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar, Atiku Abubakar, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsige Sifeta Janar na rundunar 'yan sandan kafin zaben 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel