Dino Melaye ne mai magana da yawun kwamitin takarar Atiku

Dino Melaye ne mai magana da yawun kwamitin takarar Atiku

- PDP ta nada Dino Melaye a matsayin Kakakin yakin neman zaben Atiku

- Sanatan yana cikin kwamitin da aka kaddamar mai dauke da mutane 154

Dino Melaye ne mai magana da yawun kwamitin takarar Atiku

Sanata Dino Melaye ne Kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku
Source: UGC

A jiya ne Jam’iyyar adawa ta PDP ta nada kwamitin da zai yi mata yakin neman zaben takarar Shugaban kasa a 2019. Yanzu haka an nada tsohon ‘Dan APC a matsayin wanda zai rika magana da yawun bakin wannan babban kwamitin.

Sanata Dino Melaye ne zai jagoranci bangaren magana da yawun bakin kwamitin takarar na Atiku Abubakar da Peter Obi a zaben 2019. Sanatan na Jihar Kogi ya tabbatar da wannan ne a shafin sa na Tuwita kamar yadda mu ka samu labari.

KU KARANTA: Tserewar ‘Dan takaran Gwamna zuwa APM ya rikita Shugaban APC

Dino Melaye zai rike mukamin Darektan hulda da Kungiyoyi masu zaman kan-su wanda shi ne a matsayin Kakakin yakin neman zaben Shugaban kasa na PDP. Sanatan ya bayyana cewa ya na sa ran cewa PDP za tayi nasara a kan PDP a badi.

Kwamitin yakin neman zaben na Atiki Abubakar/Peter Obi dai ya kunshi mutane har 154 wanda kusoshi ne a Jam’iyyar. Sanata Bukola Saraki shi ne Darekta Janar na tafiyar da kuma wasu manyan ‘Yan adawa na Kasar da za su dafa masa.

Rt. Hon. Yakubu Dogora; da Sanata Ike Ekweremadu su na cikin kwamitin. Haka kuma tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan da Mataimakin sa Arch. Namadi Sambo da Walid Jubrin su na wannan tsari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel