Zargin wai NPA ta boye N177b daga gwamnatin Tarayya; NPA tayi bayani dalla-dalla

Zargin wai NPA ta boye N177b daga gwamnatin Tarayya; NPA tayi bayani dalla-dalla

- An tara wa gwamnati N303b daga NPA ta gabar teku a 2017

- Gwamnati baifi rabi ta gani a asusun ta ba na bai daya

- Hadiza Bala tayi bayani yadda lamarin yake

Dalilinmu na kwange biliyoyi daga asusun gwamnati a NPA - Hadiza Bala

Dalilinmu na kwange biliyoyi daga asusun gwamnati a NPA - Hadiza Bala
Source: UGC

Majalisar Dattijai na bincikar yadda akayi gwamnati bata ji aler alert daga NPA na biliyan N177b ba daga hukumar duk da an tara N303b a shekarar 2017.

Kwamitin majalisar ya bi diddigin lamarin, inda ya baiwa hukumar kwanaki ukku kacal, ta adi inda ta kai kudaden, ko suna hannunta ko an boye a bankuna.

Ita dai shugabar hukumar, ta tabbatar da cewa, tana aiki bisa qa'ida, kuma babu wata kwange ko lakume kudade da ake yi a hukumar, inda ta kira lamarin da 'zance maras tushe'.

DUBA WANNAN: Ko yafiya da Tambawal yayi wa wasu da ake zargi da Damfara ta N15b ta hau? Kotu tace sam!

Hukumar tace, daga cikin kudaden da ta tara a bara, N303b, an kashe N205b ne a cikin ayyukan hukumar, na sayen kayayyaki, da ma tafiyar da hukumar a shekarar ta 2017.

NPA din tace N30b ce ta rage kuma ta mikawa gwamnati, a matsayin abin da yayi saura.

Sauran N177b kuwa, hukumar tace N60 daga ciki, haraji ne da ake yi wa kwastomomi yafiya don inganta harkokin da ke tafiya a aikin.

Ta kuma ce ta karo N11b ga asusun na bai daya daga cikin kudaden na bana.

Dama dai gwamnatin Kaduna ce ta bada aron Hadiza Bala Usman, watakil don ta kula da yadda Atiku Abubakar ke hada-hadarsa a Ports din ta hanyar kamfaninsa Intels, da duba watakil ko akwai cuwa-cuwa da yake yi.

Hakan kuwa baya rasa nasaba da cewa ana sa rai zai yi takara da ko Malam Nasir na APC ko Buhari a 2019.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel