Kai Madalla: Jami'o'i goma za'a sake kafawa a fadin kasar nan kwanan nan

Kai Madalla: Jami'o'i goma za'a sake kafawa a fadin kasar nan kwanan nan

- A jiya ne majalisar dattawa ta amince da samar da karin makarantun gaba da sakandire

- Makarantun sun hada da Jami'oi da kwalejoji

- Akwai kwalejin horar da malamai ma duk za'a samar

Kai Madalla: Jami'o'i goma za'a sake kafawa a fadin kasar nan kwanan nan

Kai Madalla: Jami'o'i goma za'a sake kafawa a fadin kasar nan kwanan nan
Source: Facebook

A jiya ne majalisar dattawa ta amince da samar da karin makarantun gaba da sakandire guda goma.

Akwai folitakanic guda biyar, jami'oi guda biyu, kwalejin horar da malamai guda biyu sai ta fasaha guda daya.

Makarantun sunshade da folitakanic din tarayya Kabo, jihar kano, folitakanic din tarayya a Daura, jihar Katsina, Folitakanic din tarayya a Langtang jihar Filato da folitakanic din tarayya a Kwale jihar Delta.

DUBA WANNAN: Bizar shiga Amurka: Kuyi kaffa-kaffa da Atiku, an gargadi Amurka

Sauran sun hada da Jami'ar horar da malamai ta tarayya a Aguleri, jihar Anambra, Jami'ar fasaha ta tarayya a Manchok, jihar Kaduna, kwalejin horar da malamai a Usugbenu Irrua, jihar Edo, kwalejin horar da Malamai ta tarayya a Arochukwu, jihar Abia.

Makarantun gaba da sakandire na Gwamnatin tarayya na daga cikin sama da makarantu 80 da majalisar ake jira ta amince da su.

Majiyar mu ta sanar cewa makarantun gaba da sakandire na Gwamnatin tarayya guda 80 na matakai daban daban na duba yuwuwar kirkiro su.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel