Kudaden da gwamnati da jihohi suka raba a wannan karon, duba ko nawa aka aikowa gwamnanku

Kudaden da gwamnati da jihohi suka raba a wannan karon, duba ko nawa aka aikowa gwamnanku

- Gwamnatin tarayya, jiha da kananan hukumomi sun raba Naira biliyan 788.13

- Sayar da danyen man fetur ya karu da ganga miliyan 0.82

- Gwamnatin tarayya ta samu kudin da ya kai N 299.9B

An kama iyaye da sukia bar dansu ya mutu saboda azumin kwana 40

An kama iyaye da sukia bar dansu ya mutu saboda azumin kwana 40
Source: Depositphotos

Gwamnatin tarayya, jiha da kananan hukumomi a ranar laraba sun raba Naira biliyan 788.13 a matsayin kudin tarayya na watan Octoba daga asusun Gwamnatin tarayya.

Hakan ya faru ne a taron da kwamitin kula da asusun tarayya, FAAC tayi a wannan karo.

Yace kudin da aka raba yafi Naira biliyan 698.7 da aka raba a watan Octoba da Naira biliyan 89.42.

Kudin shiga da aka samu ya kai Naira biliyan 682.16 wanda yafi Naira biliyan 569.28 da aka samu a watan da ya gabata da Naira biliyan 112.88.

A hakan kuma, siyar da danyen man fetur ya karu da ganga miliyan 0.8 wanda ya kawo kari ga kudin shigar kasar da dala miliyan 54.19.

DUBA WANNAN: China tace addinin Islama tabin hankali ne

A taka ice gwamnatin tarayya ta samu Naira biliyan 284.3 na kudin tsayayyen kudin shiga, Naira biliyan 15.14 daga VAT, Naira biliyan 0.372 daga cinikayya da wasu kasashe, wanda hakan ya tashi a Naira biliyan 299.9.

Gwamnatocin jiha sun samu Naira biliyan 144.2 daga tsayayyen kudin shiga, Naira biliyan 50.48 daga VAT, Naira biliyan 0.18 daga cinikayya, jimillar biliyan 194.9.

Kananan hukumomi sun samu Naira biliyan 111.2 daga tsayayyen kudin shiga, Naira biliyan 35.3 daga VAT, Naira biliyan 0.145 daga cinikayya, jimillar Naira biliyan 146.6.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel