2019: Majalisar wakilan tarayya ta gargadi Kudu maso Gabas akan kauracewa zabe

2019: Majalisar wakilan tarayya ta gargadi Kudu maso Gabas akan kauracewa zabe

- Majalisar wakilan tarayya ta shawarci Kudu maso Gabas da su toshe kunnuwansu ga sauraron hudubar masu rajin kafa yankin Biafra na kauracewa babban zaben 2019

- Majalisar ta ce kungiyar masu rajin kafa yankin Biafra na daga cikin manyan dalilan da ke kawo koma-baya a bangarorin siyasar shiyyar Kudu maso Gabas

- Tun farko, kwamishinan INEC na jihar Enugu, Dr Emeka Ononamadu, ya lissafa wasu matsaloli da hukumar ke fuskanta a jihar, da suka hada da rashin ruwa da wutar da lantarki

Kwamitin harkokin zabe da siyasa na majalisar wakilan tarayya ya shawarci mazauna shiyyar Kudu maso Gabas da su toshe kunnuwansu ga sauraron hudubar 'yan gani kasheni, da ke rajin kafa yankin Biafra na kauracewa babban zaben 2019.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ruwaito cewa Dr Chukwuemeka Ujam ya jagoranci wata tawaga ta mutane hudu daga cikin kwamitin zuwa wata ziyarar gani da ido ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ke jihar Enugu a ranar Alhamis.

Ujam, wanda ke wakiltar mazabar Nkanu ta Kudu da Nkanu ta Yamma a majalisar wakilan tarayya, ya yi wannan gargadin ne biyo bayan wani kira da kungiyar masu rajin kafa Biafra suka yi na cewar shiyyar Kudu maso Gabas su kauracewa zabe mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Boko Haram yanzu na dauko sojin haya daga mayakan kasashen waje - Tukur Buratai

2019: Majalisar wakilan tarayya ta gargadi Kudu maso Gabas akan kauracewa zabe

2019: Majalisar wakilan tarayya ta gargadi Kudu maso Gabas akan kauracewa zabe
Source: Twitter

Ya bukaci al'ummar da ke zaune a shiyyar Kudu maso Gabas da su fito kwansu da kwarkwatarsu don a dama dasu a zabukan masu zuwa, domin ta hakan ne kadai za su iya samar da gwamnatin da zata kare hakkokinsu da kuma cika bukatunsu.

Ya ce kungiyar masu rajin kafa yankin Biafra na daga cikin manyan dalilan da ke ka kawo komabaya a bangarorin siyasa da dama musamman wajen dakile shiyyar Kudu maso Gabas daga yin zabe, wanda kuma babbar illace ga demokaradiyyar kasar.

Ujam ya ce kwamitin ya kai ziyara ga hukumar INEC don ganewa idanuwanta irin shirye shiryen da hukumar ta yi na tunkarar babban zaben 2019, inda kuma ya tabbatar da yunkurin kwamitin na magance matsalolin da shuwagabannin hukumar a jihar suka gabatar.

Tun farko, kwamishhinan hukumar INEC na jihar Enugu, Dr Emeka Ononamadu, ya bayyana damuwarsa kan cewar hukumar ta yiwa mutane 549,326 rijista, amma ba a samu kari ba kasancewar masu rajin kafa Biafra suna hana jama'ar shiyyar yin rijista.

Ya lissafa wasu matsaloli da hukumar ke fuskanta a ofishinsu na jihar, da suka hada da rashin tsaftatacce da wadataccen ruwa da kuma rashin wutar da lantarki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel