Barin Akinlade APC ya ba Jam’iyya mamaki ainun a Ogun - Adebiyi

Barin Akinlade APC ya ba Jam’iyya mamaki ainun a Ogun - Adebiyi

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa sauya-shekar da wani na-hannun daman Gwamnan Ogun, Adekunle Akinlade yayi daga Jam’iyyar APC ya ba Jam’iyyar mai mulki mamaki matuka a Jihar.

Barin Akinlade APC ya ba Jam’iyya mamaki ainun a Ogun - Adebiyi

Shugaban APC yayi mamakin yadda Akinlade ya sauya sheka
Source: UGC

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Ogun, Derin Adebiyi ya bayyana cewa yayi matukar mamakin jin cewa Adekunle Akinlade ya bar Jam’iyyar APC ya koma Jam’iyyar adawa ta APM yayin da ake tsakiyar shiryawa zaben 2019.

Adekunle Akinlade wanda shi ne ‘Dan-takarar Gwamnan Ogun mai shirin barin gado watau Ibikunle Amosun ya fice daga Jam’iyyar ta APC mai mulki ne ya koma Jam’iyyar adawar nan ta Allied Peoples Movement, APM jiya.

KU KARANTA: Mun yi da na-sanin marawa Buhari baya a zaben 2015 - 'Yan APC

Hon. Akinlade ya bar APC ne bayan Jam’iyyar ta ba Dapo Abiodun tuta a zaben Gwamnan Jihar da za ayi a 2019. Akinlade wanda yanzu haka yake wakiltar Egbado da Ipokia a Majalisar Tarayya ya sanar da ficewar sa daga APC ne jiya.

Shugaban APC ya jijjiga kwarai da jin wannan labari inda yace yayi mamakin jin cewa Derin Akinlade ya bar Jam’iyyar a daidai lokacin da ake kokarin yin duk sulhun da ya dace. Shugaban Jam’iyyar yace zai yi maza ya tuntube sa.

A Jihar Imo ma dai, mun ji cewa Gwamnan Jihar Rochas Okorocha na shirin bijirewa Jam’iyyar APC ya kama DPP a zaben 2019. Gwamna Okorocha yace babu sulhu yanzu tsakanin sa da APC a wannan marra.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel