Yadda Hafsah ta zama Barista duk da tana fama da rashin idanu

Yadda Hafsah ta zama Barista duk da tana fama da rashin idanu

Kwanan nan ne labarin wata Makauniya da ta zama Lauya daga Arewacin Najeriya ya ratsa ko ina, ganin yadda kusan ba a saba jin mutum mai irin wannan nakasa ya jajirce har ya kai wannan mataki na karatu ba.

Yadda Hafsah ta zama Barista duk da tana fama da rashin idanu

Hafsah Sulaiman Dauda ta zama Lauya duk da rashin idanu
Source: Instagram

Legit Hausa tayi hira da wata babbar Aminiyar wannan Baiwar Allah mai suna Hafsah Sulaiman Dauda, inda ta bayyana mana yadda tayi karatun ta na tsawon shekaru har 5 har kuma ta tafi Makarantar kwarewa ta Lauyoyi.

Hafsah Sulaiman tayi karatun Firamare ne a cikin Garin Kaduna inda bayan nan ta sheka zuwa Makarantar nan ta GSS Kwali da ke Garin Abuja. Bayan kammala Sakandare ne ta samu shiga Jami’ar nan ta Ahmadu Bello.

KU KARANTA: Boko Haram su na dauko Sojin haya daga Kasashen waje - Buratai

Kamar yadda wata babbar Aminiyar ta wanda su kayi karatu tare ta bayyana mana, Hafsah ta samu kalubale a Jami’ar ta Ahmadu Bello da ke Zariya inda aka nemi a hana ta karatu saboda ganin irin babbar larurar da ta ke fama da ita.

A karshe dai, Hafsah tayi nasar ta yi karatun ta a Jami’ar da ke Kongo a cikin Zariya har ta kammala ba tare da ta gamu da wani cikas ba. Hafsah ta kan yi amfani ne da wannan irin samfari na karatu kuma ta kan gane muryar Malaman ta.

Daya daga cikin Kawayen ta, tana cewa ta kan manta cewa Hafsah ba ta gani da idanun ta saboda yadda ta ke komai kamar sauran mutane. Malama Hafsah dai mace ce mai kokari da jajircewa fiye da sauran mutane masu idanu inji Aminan ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel