Yaki da rashawa: Yan majalisu sun gayyaci Ministan Buhari akan badakalar cin hanci da rashawa

Yaki da rashawa: Yan majalisu sun gayyaci Ministan Buhari akan badakalar cin hanci da rashawa

Kwamitin majalisar wakilai akan harkokin sufurin kasa ta gayyaci ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya gurfana gabanta domin ya amsa tambayoyi game da wasu badakaloli da suka taso daga ma’aikatarsa, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito shugaban kwamitin, Abdulmuminu Jibrin ne ya bayyana haka cikin wata hira da yayi da ita a ranar Alhamis 29 ga watan Nuwamba a babban birnin tarayya Abuja, inda ya bayana mata irin tuhumar da suke yi ma Amaechi.

KU KARANTA: An fasa kwai: Babban dalilin da yasa likitocin Najeriya suke hijira zuwa kasashen waje

Dan majalisa Abdulmuminu Jibrin ya bayyana cewa majalisar ta gayyaci Amaechi ya gurfana a gabanta ne saboda zargin yin kaca kaca da tsarin gudanar da aikin gwamnati, da kuma zargin tafka cin hanci da rashawa.

A cewar Abdulmuminu Jibrin, majalisar ta samu korafe korafe da dama da mutane daban daban suka turo game da ministan, don haka suke ganin ya dace su binciki wadannan korafe korafe ta yadda zasu gabo bakin zarin.

“Mun samu ingantattun korafe korafe da dama daga yan Najeriya masu karfi game da ministan, daga cikinsu akwai zarge zarge da suka shafi karya dokokin aiki, kokarin kawar da hankalin gwamnatin tarayya, da ma zargin cin hanci da rashawa.

“Don haka muka gayyaceshi ya bayyana gaban kwamitin domin mu sauraran bayanansa da martanin da zai bayar game da zarge zargen ta yadda zamu mika ma majalisa rahoton binciken da muka yi.

"Muna ganin idan har gwamnati zata ranto dala miliyan Tara daga kasar Sin domin wannan aiki na shimfida layin dogo, ga kuma kudin da gwamnatin Najeriya ta biya daga nata bangaren, to lallai ya zama wajibi yan Najeriya su san inda kudaden suke zuwa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel