Korarrun ma’aikatan jahar Kaduna sun shiga hannu bayan an kamasu suna yi ma El-Rufai Al-kunut

Korarrun ma’aikatan jahar Kaduna sun shiga hannu bayan an kamasu suna yi ma El-Rufai Al-kunut

Wasu tsofaffin ma’aikatan jahar Kaduna da gwamnatin Malam Nasir Ahmad El-Rufai sun fada komar jami’an hukumar Yansandan Najeriya a sanadiyyar shirya addu’ar Al-kunuti a jahar, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta bayyana cewa korarrun ma’aikatan sun shirya addu’ar ne saboda gwamnatin jahar Kaduna ta ki biyansu hakkokinsu na barin aiki tun bayan da gwamnatin ta sallamesu daga aikin.

KU KARANTA: An fasa kwai: Babban dalilin da yasa likitocin Najeriya suke hijira zuwa kasashen waje

Ita dai wannan addu’ar ana yinta ne ga shuwagabannin azzalumai, a duk lokacin da zaluncin shuwagabannin ya tsananta kuma babu wata mafita, don haka sai a taru a gudanar da sallar nafila, a karanta doguwar addu’a da nufin Allah ya kawo mafita.

Shugaban kungiyar ma’aikatan da gwamnatin jahar Kaduna ta sallama, Emmnuel Dogo, ya tabbatar da kama mutanen nasa a ranar Alhamis 29 ga watan Nuwamba, inda yace gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai ne ya bada umarnin a kamasu.

A cewar Dogo yace dolece ta sanya suka yanke shawarar gudanar da alkunuti saboda talauci da yunwa ya damesu, don ko kulawa da iyalansa ya gagara saboda gwamnatin ta kasa biyansu hakkokinsu tun bayan data suka bar aiki.

“Duk kokarin da muka yin a ganin gwamnatin ta biyamu kudadenmu yaci tura, don haka abinda ya rage mana kawai shine mu gudanar da addu’a don mu fada ma Allah ubangiji. Saboda wannan adduar ne gwamnan ya bada umarnin a kama mutanenmu a Zaria.

“An fara gayyatarsu su zuwa babban ofishin Yansandan jahar Kaduna, daga bisani aka mayar dasu ofishin yansanda na CID, a can aka rikesu, munyi ta zuwa CID don jin laifinsu, amma suka ce mana zasu gurfanar dasu a gaban kotu.” Inji shi.

Sai dai duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin kaakakin rundunar Yansandan jahar Kaduna game da lamarin ba yiwu ba sakamakon majiyarmu bata sameshi a wayar tarho ba, kuma bai sakon karta kwana da ta tura masa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel