Deji Adeyanju: An nemi Gwamnati ta gaggauta sakin ‘Yan gwagwarmaya

Deji Adeyanju: An nemi Gwamnati ta gaggauta sakin ‘Yan gwagwarmaya

Mun samu labari daga Birnin Tarayya Abuja cewa Kungiyar nan ta Amnesty International tayi tir da damke wasu Matasa ‘Yan gwagwarmaya 3 da Jami’an tsaro su ka yi kwanan nan a cikin Najeriya.

Deji Adeyanju: An nemi Gwamnati ta gaggauta sakin ‘Yan gwagwarmaya

Amnesty International sa baki game da tsare masu zanga-zanga
Source: UGC

Kwanan nan ne ‘Yan Sanda su kayi ram da wasu mutum 3 a Najeriya da su ke zanga-zanga game da abin da yake faruwa a Majalisar dokokin Jihar Akwa-Ibom. Wadanda aka kama su ne; Deji Adeyanju; Daniel Abobama da kuma Boma Williams.

Adeyanju da sauran ‘Yan uwan na sa, sun koka ne da yadda Jami’an tsaro su ka saki layi, su ke neman tada zaune tsaye a Majalisar Jihar Akwa-Ibom bayan wasu ‘Yan Majalisa sun sauya-sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulkin kasa.

KU KARANTA: An fadawa Amurka ta guji ba Atiku Abubakar takardun biza

Amnesty International ta reshen Najeriya ta bayyana cewa daure Mista Adeyanu da sauran takwarorin sa har su 2 da aka yi, yana cikin keta hakkin Bil–Adama kuma kokarin hana masu gwagwarmaya da Hukumomin Gwamnati sakat a Najeriya.

Kungiyar wanda tayi fice wajen kwato hakkin Jama’a ta nemi Jami’n tsaro na 'Yan Sanda su gaggauta sakin wadannan mutane. Jami’an tsaro dai su na zargin su da aikata laifuffuka da su ka shafi sashe na 96, 113, 114, 152, 183 da na 391 na final kwad.

Amnesty International dai tace a tsarin damukaradiyya, kowa yana da damar gudanar da zanga-zanga. Sai dai Jami’an tsaro su na ganin ‘Yan kungiyar na Concerned Nigerians sun wuce gona da iri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel