Ina tare da Buhari a sama; amma a Imo Jam’iyyar DPP za mu zaba - Okorocha

Ina tare da Buhari a sama; amma a Imo Jam’iyyar DPP za mu zaba - Okorocha

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Imo mai shirin barin-gado watau Mai Girma Rochas Okorocha ya bayyana cewa zai marawa ‘Dan takarar Jam’iyyar DPP a zaben Gwamnan Jihar sa da za ayi a 2019.

Ina tare da Buhari a sama; amma a Imo Jam’iyyar DPP za mu zaba - Okorocha

Gwamna Okorocha zai marawa Surukin sa baya a zaben Imo
Source: Facebook

Today.ng ta rahoto Rochas O. Okorocha ya nuna cewa zai goyi bayan Surukin sa Uche Nwosu wanda Jam’iyyar APC ta hana takarar Gwamna a Jihar Imo. Yanzu dai Uche Nwosu ya tsaya takara ne a karkashin Jam’iyyar adawa ta DPP.

Uche Nwosu wanda na-hannun daman Gwamna Okorocha ne, da kuma wasu manyan Hadiman Gwamnan da kuma ‘Yan Majalisun dokokin Jihar Imo sun fice daga Jam’iyyar APC sun koma DPP domin yin takara a zaben 2019.

KU KARANTA: 2019: Babu maganar sulhu a Jihar Imo inji Okorocha

Fitaccen Gwamnan ya tabbatar da cewa duk da zai marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a zaben 2019, zai yi bakin kokarin sa ne wajen ganin Surukin sa yayi nasarar lashe kujerar Gwamna a Jam’iyyar ta DPP a zabe mai zuwa.

Haka kuma shi Gwamnan zai yi takarar kujerar Sanatan Yankin Orlu na Jihar Imo a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki. Gwamnan yana ganin APC ba tayi wa ‘Dan takarar sa adalci ba na hana sa tikiti don haka ya sauya-sheka.

Kwanaki Shugaban Gwamnonin na Jam’iyyar APC yayi wa Shugaba Buhari bayanin abubuwan da Oshiomhole yayi a Jihar ta Imo. Gwamnan yana zargi Shugaban na APC ne ya jefa Jam’iyyar cikin matsala.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel