Lalong ya amince da daukar ma’aikata 1,661

Lalong ya amince da daukar ma’aikata 1,661

Hukumar ma’aikatan gwamnatin jihar Plateau ta bayyana cewa Gwamna Simon Lalong na jihar ya amince da daukar sabbin ma’aikata 1,661 a fadin jihar aikin gwamnati.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta bakin shugabanta, Cif Dajung Fompun lokacin wani taron manema labarai a ranar Talata.

“Ma’aikata da ke rabewa tare da gwamnatin jihar ma za su samu damar da za su shiga cikin diban ma’aikatan, saboda a farkon wannan shekarar kimanin ma’aikata da ke rabewa 300 aka kwasa a ma’aikatar muhalli,” inji shi.

Lalong ya amince da daukar ma’aikata 1,661

Lalong ya amince da daukar ma’aikata 1,661
Source: Depositphotos

An tattaro cewa a ma’aikatar ilimi za’a kwashi ma’aikata da ba koyarwa za su yi ba guda 161, hukumar ma’aikatar asibiti na Plateau zata kwashi mutane 108, ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati 77, sannan fannin noma 62.

KU KARANTA KUMA: Wadanda suka sauya sheka daga APC sun yi danasanin marawa Buhari baya a 2015

Hukumar aikin hajji da na Kirista za su samu tara.

Hukumar kare yancin nakasassu 54, yayinda majalisar dokokin Plateau zata kwashi 21.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel