Ya zama dole a tsige Sufeto Janar din ‘yan sandan Kasa kafin zabukan 2019 - Atiku

Ya zama dole a tsige Sufeto Janar din ‘yan sandan Kasa kafin zabukan 2019 - Atiku

Tsohon mataimakain shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira da a tsige Sufeto Janar din ‘yan sandan kafin zabukan 2019.

Atiku ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da kwamitin kamfen din sa wanda shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki zai shugabanta.

A cewar dan takarar shugaban kasar ya zama dole kwamitin su tabbata da an tsige Sufeto Janar Idris kafin zabe domin babu alamar zai yi adalci a aikin sa.

Ya zama dole a tsige Sufeto Janar din ‘yan sandan Kasa kafin zabukan 2019 - Atiku

Ya zama dole a tsige Sufeto Janar din ‘yan sandan Kasa kafin zabukan 2019 - Atiku
Source: Twitter

Ya ce: “Dole ne mu tabbatar da an tsige sufeto janar din ‘yan sandan kasa kafin zabukan 2019. Wannan yana daga cikin manyan abubuwan da zamu sanya a gaba.

KU KARANTA KUMA: Wadanda suka sauya sheka daga APC sun yi danasanin marawa Buhari baya a 2015

“Bayan haka jam’iyyar APC ta koma sai tsikarar mu take gaba-gadi saboda gazawa da tayi na kawo sauyi na gari a kasar nan tun bayan hawanta karagar mulki a 2015.

“Za mu tunkari jam’iyya ce wato APC da take so ta ci gaba da mulki ko ta halin kaka. Wannan gwabzawa da za a yi a 2019 zai fi dukkan zabukkan da aka yi tun 1999.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel