Yan sanda sun kama maza karuwai masu damfara a Kano

Yan sanda sun kama maza karuwai masu damfara a Kano

Rundunar `yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta kama wasu mutane biyu maza da ake zargin 'yan luwadi ne, wadanda ke amfani da kafofin sada zumunta suna tallata kansu.

Binciken da rundunar ta yi ya nuna cewa mazajen su kan fara ne data hanayar kulla zumunci da mutane, bayan haka sai su nemi a yi lalata da su, har su kan yi barazanar bata wa mutum suna idan bai ba su hadin kai ba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Sufurtanda Majiya ya ce matasan sun yi ta bibiyar wani attajiri har suka kulla alaka da shi, sannan suka fara yi masa barazana.

Yan sanda sun kama maza karuwai masu damfara a Kano

Yan sanda sun kama maza karuwai masu damfara a Kano
Source: Depositphotos

"Daga farko sun fara kiran shi ne suna yi masa godiya a matsayin makwabci ne ko mai hali da yake taimakawa. Daga karshe kuma sai suka bi shi da cewar ya ba su kudi. Ya ce kudin me? Sai suka ce kudin da ya yi amfani da shi," in ji Majiya.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya dawo Najeriya bayan halartar taro a kasar Chadi

'Yan sandan sun ce mutanen sun yi wa mutumin barazana cewa idan bai ba su kudi ba to za su bata masa suna a shafukan sada zumunta, cewa ya yi lalata da su.

A cewar Majiya anyi nasarar kama su ne bayan an tsaurara bincike akansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel