'Yar sanda da mutum biyu sun mutu bayan cin abincin dare

'Yar sanda da mutum biyu sun mutu bayan cin abincin dare

Wata babbar jami'ar hukumar 'yan sanda tare da su 'yan uwanta biyu sun mutu a garin Osogbo, babban birnin jihar Osun, da safiyar yau bayan cin abincin wani abinci kafin su kwanta.

'Yar sandan mai suna Mary Samuel, da ke zaune a wani gidan haya a rukunin gidajen Oloosaoko a yankin Oja-Oba, ana zargin ta mutu ne bayan cin abincin da ake zargin ya gurbata a daren ranar Laraba..

Majiyar mu ta bayyana ma na cewar makwabtan 'yar sandan ne su ka ji yarinyar ta na ta kuka, amma da su ka zo don ganin abinda yake faruwa sai su ka iskar gawar ta zaune kan kujera.

Sai dai, har yanzu ba a tantance mene ne ya jawo mutuwar ta ba.

'Yar sanda da mutum biyu sun mutu bayan cin abincin dare

Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa; Jimoh Moshood
Source: Facebook

Wata makwabciyar Mary ta shaidawa majiyar mu cewar, "da daddare na ji kukan yarinyar ta ya yi yawa, sai na fita don na bincika abinda ke faruwa. Nayi bugu ma ta kofa amma shiru, babu amsa. Sai na leka ta taga, sai na hange ta kwance kamar tana cikin yanayin barci mai nauyi amma kusan rabinta tsirara.

"Sai na koma na taso jama'a, mu ka zo muka balle kofa mu ka shigo, sai mu ka ganta zaune a kan kujera, rike da cocilan a hannunta, amma an zare ma ta rai.

DUBA WANNAN: 2019: Mata 62 ne ke takara a Kano - INEC

"Nan da nan mu ka gaggauta sanar da 'yan sanda. Bayan sun zo ne su ka fito da gawar mutane uku daga gidan, ciki har da Anti Mary. Amma an garzaya da 'yar uwar ta da aka samu tana numfashi sama-sama zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Akintola University dake Osogbo.

Shaidar gani da ido ya ce kwamishinar 'yan sanda ta jihar, Mista Fimihan Adeoye, ya ziyarci gidan da Mary ta mutu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel