Najeriya ta shigo Litar Man fetur 4.37bn cikin watanni 3 kacal - NBS

Najeriya ta shigo Litar Man fetur 4.37bn cikin watanni 3 kacal - NBS

Hukumar kididdigar Alkaluma ta Najeriya watau NBS, National Bureau of Statistics, ta bayyana cewa Najeriya ta shigo da adadin Lita Biliyan 4.37 ta Man fetur da ma'adanansa cikin kasar nan a 3 bisa 4 na watannin shekarar 2018.

Kamar yadda Alkaluma suka bayyana, man fetur da dangin ma'adanansa na Lita Biliyan 4.37 sun shigo cikin kasar a tsakanin watan Yuli zuwa Satumba na wannan shekara.

Kididdigar kamar yadda hukumar NBS ta fitar ta bayyana adadin Litar man fetur da ma'adanansu suka shigo cikin kasar nan kamar haka: Litar Man Fetur miliyan 873.72, Kalanzir; Miliyan 312.71, Makamashin Gas na manyan Motoci da Injina wautau Diesel; Miliyan 873.72.

Kazalika Man Jiragen sama Lita Miliyan 212.80 sun shigo kasar nan da kuma Lita Miliyan 162.37 ta makamashin gas a tsakanin wannan lokuta na watanni uku.

Najeriya ta shigo Litar Man fetur 4.37bn cikin watanni 3 kacal - NBS

Najeriya ta shigo Litar Man fetur 4.37bn cikin watanni 3 kacal - NBS
Source: Facebook

Cikin wani rahoton da hukumar NBS ta fitar ya bayyana cewa, shigowar man fetur ta kasance mafi girma a watan Satumba inda aka ketaro da Lita Biliyan 1.59 yayin da Makamashin gas na Diesel da Kalanzir suka ciri tuta ta mafi girma a watan Yuli da kuma na Agusta.

KARANTA KUMA: Rushewar Jami'o'i muke gujewa, ASUU ta shaidawa Iyaye, 'Dalibai dalilinta na Yajin Aiki

Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito, kididdigar ta zayyana yadda jihar Legas ta kere sauran jihohin Najeriya da aka wadata ta da Litar man fetur miliyan 547, sai kuma jihar Kano mai Lita miliyan 277, jihar Neja da ta samu wadatuwa da Lita Miliyan 163 da kuma jihar Ogun da ta samu wadatuwar Lita Miliyan 155 cikin watanni uku.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wata mujallar lura da hada-hadar kasuwanci ta business a.m, ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta batar da Naira Biliyan 900 wajen shigo da man fetur da ma'adanansa cikin kasar nan a watanni uku kacal.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel