2019: Mata 62 ne ke takara a Kano - INEC

2019: Mata 62 ne ke takara a Kano - INEC

A kalla mata 62 ne ke takarar kujeru daban-daban a zabukan shekarar 2019 a Kano,a cewar kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a jihar, Riskuwa Shehu.

Mista Shehu ya sanar da hakan ne a yau, Alhamis, ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) yayin da yake bayar da kiyasin adadin fam din 'yan takara da hukumar ta karba a jihar Kano.

Shehu ya bayyana cewar ofishin INEC a jihar Kano ta karbi sunayen mutane 74 dake takarar kujerar Sanata a sanatoriya uku a jihar.

A cewar kwamishinan, daga cikin 'yan takarar kujerar Sanatan 74 da jam'iyyu 32 su ka mika, biyu ne kawai mata.

2019: Mata 62 ne ke takara a Kano - INEC

2019: Mata 62 ne ke takara a Kano - INEC
Source: Depositphotos

Sannan ya kara da cewar daga cikin mutane 401 da ke takarar kujerar majalisar wakilai, 17 ne kacal mata.

DUBA WANNAN: Abu biyu kacal gwamnatin Buhari ta samar - PDP

Kwamishinan ya kara da cewar daga cikin mutane 718 da ke takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kano da jam'iyyu 37 su ka mika, 37 ne kawai mata.

Da yake amsa tambaya a kan kwatanta zaben tsakiyar zango a kasar Amurka da na Najeriya, Shehu ya ce a bari har sai bayan kammala zabukan shekarar 2019 tukunna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel