Rushewar Jami'o'i muke gujewa, ASUU ta shaidawa Iyaye, 'Dalibai dalilinta na Yajin Aiki

Rushewar Jami'o'i muke gujewa, ASUU ta shaidawa Iyaye, 'Dalibai dalilinta na Yajin Aiki

Kungiyar Malaman Jami'o'in Najeriya ta ASUU, ta nemi fahimtar dalibai gami da Iyaye kan matsayarta inda ta bayyana cewa kawowa yanzu ba bu ranar janye yajin aikin ta domin ci gaba da jajircewa wajen ceto makomar Jami'o'in kasar nan.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ruwaito, kungiyar ta nemi Iyaye da Dalibai wajen fahimtar dalilin hukuncin ta na ci gaba da yajin aiki domin gujewa zangwayewa da rushewar jami'o'in kasar nan.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, shine ya bayyana wannan kira ga Dalibai da kuma Iyaye yayin ganawarsa da manema labarai yau Alhamis can jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Malaman Jami'o'in kasar nan a ranar 5 ga watan Nuwamba sun afka yajin aiki gadan-gadan sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen cika alkawurra da kuma yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar tun a shekarar 2009 da ta gabata.

Rushewar Jami'o'i muke gujewa, ASUU ta shaidawa Iyaye, 'Dalibai dalilinta na Yajin Aiki

Rushewar Jami'o'i muke gujewa, ASUU ta shaidawa Iyaye, 'Dalibai dalilinta na Yajin Aiki
Source: Twitter

Malaman jami'o'in a halin yanzu na kuma kira ga gwamnatin tarayya kan tabbatar da cika alkawuranta da yarjejiyar da ta kulla a shekarar 2017 da ta gabata da suka hadar da inganta harkokin gudanarwa da jin dadin Malamai da inganta wuraren karatu na Dalibai a jami'o'in kasar nan.

Farfesa Ogunyemi ya bayyana cewa, wannan yajin aiki ba ya da wata manufa ko nasaba ta kusa ko nesa wajen muzgunawa Dalibai, Iyaye da dukkanin masu ruwa da tsaki, illa iyaka jajircewarsu ta ceto jami'o'in kasar nan daga zagwanyewa.

KARANTA KUMA: Duk da zargin rashawa, Wakilan jihar Kano na Majalisar Tarayya sun goyi bayan tazarcen Gwamna Ganduje

A yayin da yajin aiki shi kadai ne yaren da gwamnatin kasar ke fahimta wajen biyan bukatun al'umma, Farfesa Ogunyemi ya nemi gwamnatin tarayya da kuma na jihohi akan sauya nazarinsu wajen kara kaimin inganta tare da tabbatar da ci gaban jami'o'in kasar nan.

A sanadiyar haka kungiyar take kira musamman ga Dalibai da kuma Iyaye kan sanya wannan lamari bisa ma'auni na fahimta da ta yiwu yajin aikin zai kai wani lokaci mai tsawo sakamakon rashin jituwa tsakanin ta da gwamnatin tarayya na cika alkawurran da ta dauka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel