Ko yafiya da Tambawal yayi wa wasu da ake zargi da Damfara ta N15b ta hau? Kotu tace sam!

Ko yafiya da Tambawal yayi wa wasu da ake zargi da Damfara ta N15b ta hau? Kotu tace sam!

- Kotun daukaka kara ta soke sassaucin da aka yiwa mutane biyu da ake zargin da satar Naira biliyan 15

- Ana zargin mutanen biyu da kwashe kudin jihar Sokoto

- Masu shari'ar sunce bai kamata ayi sassauci ga wadanda baa kai gaban kuliya ba

Ko yafiya da Tambawal yayi wa wasu da ake zagi da Damfara ta N15b ta hau? Kotu tace sam!

Ko yafiya da Tambawal yayi wa wasu da ake zagi da Damfara ta N15b ta hau? Kotu tace sam!
Source: Twitter

Masu shari'a biyar dake kotun daukaka kara ta jihar Sakkwato wadanda mai shari'a Hannatu Sankey, a ranar Alhamis sun soke sassaucin da akayi wa wasu mutane biyu.

Mutane biyun dai hukumar yaki da rashawa ce ta zarge su satar kudi har Naira biliyan 15 na gwamnatin jihar.

Gwamna Tambuwal ne ya bada sassaucin ga tsohon sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Muhammad Maigari Dingyadi da Isa Sadiq Achida, bayan kuma basu riga sun tsaya gaban kuliya ba.

Amma a hukuncin da daukaka karar da hukumar yaki da rashawa tayi, kotun tace bai dace gwamnan ya basu sassauci ba bayan suna gaban kuliya kuma ba a riga an yanke hukunci ba.

Masu shari'ar sunce har yanzu mutane biyun masu gaskiya ne har sai kotu ta yanke hukunci.

Don haka kotu ta umarci wadanda ake zargi dasu fuskanci shari'a akan abinda ake zargin su da ita.

DUBA WANNAN: Kasar Sin ta kira addinin Islama da sunan banza

Kotun daukaka karar ta bukaci wadanda ake zargin dasu gwada babbar kotun jihar.

Idan za'a tuna wadanda ake zargin suna fuskantar shari'a ne tare da tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, akan Naira biliyan 15 na jihar wanda mai shari'a Bello Abbas ya saki tare da Alhaji Tukur Alkali, Bello Isah da Alhaji Halilu Modachi.

An sake su bayan da suka gabatar da shaida cewa a sake su saboda gwamnan jihar Sakkwato yayi musu sassauci.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel