Duk da zargin rashawa, Wakilan jihar Kano na Majalisar Tarayya sun goyi bayan tazarcen Gwamna Ganduje

Duk da zargin rashawa, Wakilan jihar Kano na Majalisar Tarayya sun goyi bayan tazarcen Gwamna Ganduje

Mun samu rahoton cewa wasu daga cikin wakilan jihar Kano a majalisun tarayyar Najeriya, sun bayyana goyon bayansu tukuru kan gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje dangane da zargi da tuhumarsa da laifin rashawa.

'Yan Majalisar sun kuma bayyana goyon bayan su tare da bayar da sahalewa ta aminci dangane da tazarcen gwamnan yayin da yake sake takarar kujerar sa a babban zabe na 2019.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, 'yan Majalisar sun kuma yabawa gwamnan dangane da kwazonsa akan karagar mulki ta jihar Kano da a cewar su ya cancanci tazarce na jagorancin al'ummar Kanon Dabo.

Ganduje a halin yanzu na ci gaba da fuskantar dambarwa ta zargin rashawa tun yayin bayyanar wani faifan bidiyo da ya bayyana yadda gwamnan ke karbar na goro a hannun wasu 'yan kwangila da ya janyo babatu da cecekuce a zaurukan sada zumunta.

Duk da zargin rashawa, Wakilan jihar Kano na Majalisar Tarayya sun goyi bayan tazarcen Gwamna Ganduje

Duk da zargin rashawa, Wakilan jihar Kano na Majalisar Tarayya sun goyi bayan tazarcen Gwamna Ganduje
Source: Depositphotos

Sai dai gwamnan ya musanta wannan zargi yayin da Kotu ta bayar da umarnin dakaci ga majalisar dokoki ta jihar akan bincikar wannan zargi.

Yayin ganawarsu da manema labarai a yau Alhamis 'Yan Majalisar sun bayyana amincinsu ga Gwamna Ganduje inda suka bayyana cewa, wannan zargi da tuhumu wata kitirmumura ce ta 'yan adawa da manufa ta shafa ma sa bakin fenti.

'Yan Majalisar da suka jaddada goyon bayan su ga Gwamnan sun hadar da; Sanata Kabiru Gaya da kuma Sanata Barau Jibrin baya ga mambobi 14 ma su wakilcin Kano a majalisar wakilai da suka rattaba hannu kan wannan sanarwa.

Mambobin Majalisar wakilan da suka yabawa kwazon gwamna Ganduje kan ci gaban jihar tare da bayar da sahalewar su kan tazarcensa sun hadar da; Abdulmumin Jibrin, Nassiru Ahmed, Tijjani Jobe, Alhassan Doguwa, Abdullahi Gaya, Badamasi Ayuba da kuma Bashir Baballe.

KARANTA KUMA: 2019: 'Yan Najeriya na ci gaba da marmarin kaɗawa Atiku 'Kuri'un su - PDP

Sauran 'yan Majalisar sun dara da Munir Dan Agundi, Aminu Suleiman, Mustapha Dawaki, Sulaiman Aliyu Romo, Muhammad Wudi, Mukhtar Chiromawa da kuma Sani Bala.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, ta bayar da sanarwa fara gudanar da bincike kan zargin karbar rashawa da ake yiwa gwamnan jihar Kano Ganduje.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel