Yanzu-yanzu: An kara samun sansanin horon soji na bogi a jihar PDP

Yanzu-yanzu: An kara samun sansanin horon soji na bogi a jihar PDP

Hukumar Sojin Najeriya ta ce jami'anta sun gano wani haramyaccen sansanin bayar da horo na fada da bindiga a Nonwa Gbam (sansanin horas da 'yan yiwa kasa hidima) a karamar hukumar Tai da ke jihar Rivers.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kungiyar dattawan Ogoni sun zargi Ma'aikatar Muhalli na Kasa da kawo dakarun sojoji zuwa garuruwan Ogoni domin samar da tsaro yayin da ake aikin tsaftace garuruwan da danyen man fetur ya gurbata.

Mataimakin Direktan yada labarai na sojin, Aminu Iliyasu ya ce dakarun sojojin sun gano sansanin bayar da horon ne yayin da suke kewaya garin.

"Dakarun sojin sun sama matasa fiye da 100 da ake bawa horo irin na soji," inji shi.

Yanzu-yanzu: Gwamna Wike ya harzuka bayan soji sun gano haramtaccen sansanin bayar da horo a Rivers

Yanzu-yanzu: Gwamna Wike ya harzuka bayan soji sun gano haramtaccen sansanin bayar da horo a Rivers
Source: Depositphotos

"Hukumar Sojin tare da hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro sun fara gudanar da bincike domin binciko wadanda ke daukan nauyin 'yan bindigan da kula da sansanin."

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da sanarwar fara daukar aiki

Ya kara da cewa sojin ta gano haramtattun sansanin bayar da horo masu kamanceceniya da wannan a jihohin Benue da Taraba a farkon wannan shekarar kuma an dauki mataki a kansu saboda tattabat da tsaro.

A martaninsa ga wannan lamarin, Gwamnan jihar, Nyesome Wike ya ce Hukumar Sojin Najeriya ta zama makami da 'yan siyasa ke amfani da ita domin kuntatawa talakawan Najeriya.

Ya ce tarwatsa sansanin bayar da horon na jihar Rivers da Soji su kayi rashin sanin ya kamata ne kuma zai iya haifar da rashin zaman lafiya a jihar.

"Sojin ba su damu da yadda Boko Haram ke kashe sojojin mu a Borno ba. Sun mayar da hankali ne wajen tayar da fitina a jihar Rivers.

"Idan ba ku son a zauna lafiya a Rivers, toh sauran sassan Najeriya ma ba za a samu zaman lafiya ba. Suna son suyi amfani da bindigogin su domin kashe mu," inji Wike.

Wike ya ce gwamnatin jihar ta hada gwiwa da Hukumar Yan sanda, DSS da sauran hukumomin gwamnatin tarayya wajen kafa 'yan bangar jihar Rivers 'Rivers State Neighbourhood Safety Corps Agency.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel