Rikicin APC a jihar Imo: Babu sulhu - Okorocha

Rikicin APC a jihar Imo: Babu sulhu - Okorocha

- Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya ce rikicin jam'iyyar APC na jiharsa ta kai matsayin da ba zai yiwu ayi sulhu ba

- Ya ce an hana al'ummar jihar su tsayar da dan takarar gwamnan da suke kauna a zaben 2019

- Sai dai Okorocha ya ce zai cigaba da kasancewa dan jam'iyyar APC mai biyaya kuma zai yi takarar kujerar sanata na mazabar Imo ta yamma a jam'iyyar

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya ce rikice-rikicen da ke afkuwa a jam'iyyar APC a jihar ya wuce matakin da za ayi sulhu.

Daily Trust ta ruwaito cewa ya ce an hana al'ummar jihar tsayar da dan takarar gwamna da suke so a 2019, kuma a halin yanzu babu yadda za ayi jam'iyyar da gyra kura-kuren da tayi.

Rikicin APC a jihar Imo: Babu sulhu - Okorocha

Rikicin APC a jihar Imo: Babu sulhu - Okorocha
Source: Depositphotos

Legit.ng ta gano cewa a yayin da ya ke tattaunawa da kwamitin sulhu na APC karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje a ranar Alhamis, 29 ga watan Nuwamba, Okorocha ya ce mutane jihar sunyi gaba.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da sanarwar fara daukar aiki

Sai dai shi ya ce har yanzu tare da da jam'iyyar APC kuma zai yi takarar kujerar sanata na mazabar Imo ta yamma a karkashin jam'iyyar.

An ruwaito cewa kwamitin sulhun na cigaba da ayyukanta na kokarin sulhunta fusattatun yan jam'iyyar a yayin rubuta wannan rahoton.

A wani rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa dan takarar da gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun yake son ya gaje shi, Adekunle Akinlade ya fice daga APC ya koma jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM).

An ruwaito cewa Akinlade tare da wasu mutane uku sun fice daga APC ne bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani da aka gudanar a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel