A shirye nake mu fafata a taron muhawarar shugaban kasa - Atiku ya shaidawa Buhari

A shirye nake mu fafata a taron muhawarar shugaban kasa - Atiku ya shaidawa Buhari

- Atiku Abubakar, ya shaidawa shugaban kasa Buhari cewar a shirye yake su fafata a taron muhawar shugaban kasa da aka shirya don fuskantar zaben 2019

- Ya kuma ce ya shirya gudanar da yakin zabe mai cike da bayyana manufofi ba wai yakin zabe na kaiwa juna farmaki da kalaman batanci ko aibatawa ba

- Dan takarar shugaban kasar na PDP ya kuma bukaci Buhari da ya sanya hannu kan sake fasalin dokar zabe da majalisun tarayya suka gabatar masa

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP ya shaidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewar a shirye yake su fafata a taron muhawar shugaban kasa da aka shirya don fuskantar zaben 2019.

Abubakar ya shaidawa Buhari hakan a ranar Alhamis a bukin kaddamar da kungiyar yakin zaben shugaban kasa karkashin jam'iyyar a Abuja.

Ya kuma ce ya shirya gudanar da yakin zabe mai cike da bayyana manufofi ba wai yakin zabe na kaiwa juna farmaki da kalaman batanci ko aibatawa ba.

KARANTA WANNAN: Daga karshe: EFCC ta mikawa 'First Bank' motoci 116 da gidaje 20

A shirye nake mu fafata a taron muhawarar shugaban kasa - Atiku ya shaidawa Buhari

A shirye nake mu fafata a taron muhawarar shugaban kasa - Atiku ya shaidawa Buhari
Source: Depositphotos

"An bukace ni da in tunadar da APC da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewar ni Atiku Abubakar, a shirye nake mu fafata a taron muhawarar," a cewarsa.

Abubakar ya kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsige Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda kafin babban zaben 2019. Wannan kuwa baya rasa nasaba da yadda jam'iyyar hamayyar take zargin Idiris da sauyin ra'ayi, musamman idan aka zo batun zabe.

Dan takarar shugaban kasar na PDP ya kuma bukaci Buhari da ya sanya hannu kan sake fasalin dokar zabe da majalisun tarayya suka gabatar masa, a hannu daya kuma yana shawartar yan siyasa da su kasance masu nuna dattako lokacin yakin zabe.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel