Shugaban masu rinjaye a majalisar Ogun da wasu 3 sun sauya sheka daga APC

Shugaban masu rinjaye a majalisar Ogun da wasu 3 sun sauya sheka daga APC

Mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) guda hudu a majalisar dokokin jihar Ogun a ranar Alhamis, 29 ga watan Nuwamba sun sauya sheka zuwa Allied Peoples Movement (APM).

Yan majalisar sun sanar da sauya shekar nasu ne a wasiku daban-daban wanda akakin majalisar, Mista Suraj Adekunbi ya karata a lokacin zaman majalisar a Abeokuta.

Masu sauya shekar sune, shugaban masu rinjaye Idowu Olowofuja; Mista Adeyinka Mafe (Sagamu1); the Chief Whip, Ganiyu Oyedeji (Ifo11); da kuma Tunde Sanusi (Obafemi Owode).

Shugaban masu rinjaye a majalisar Ogun da wasu 3 sun sauya sheka daga APC

Shugaban masu rinjaye a majalisar Ogun da wasu 3 sun sauya sheka daga APC
Source: Depositphotos

Yan majalisar sun bayyana cewa sun bar APC ne saboda rashin adalcin da jam’iyyar ta yi a lokacin zaben fidda gwaninta.

Sun bayyana cewa sun yanke wannan hukunci ne bayan tuntubar mazabarsu da magoya bayansu.

KU KARANTA KUMA: Bacewar biliyoyin naira: Majalisar dattawa za ta bincike hukumar kula da tashoshin ruwa

Oyedeji a wasikarsa ya bayyana cewa duk da sauya shekarsa, zai marawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari baya a zaben 2019 sannan cewa zai ci gaba da marawa Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun baya.

A nashi martanin, kakakin majalisar ya yi masu fatan alkahiri a sabuwar jam’iyyarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel