2019: PDP ta kaddamar da addu’o’i da azumin kwana 7 don yin zabe cikin zaman lafiya a Enugu

2019: PDP ta kaddamar da addu’o’i da azumin kwana 7 don yin zabe cikin zaman lafiya a Enugu

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Enugu ta kaddamar da addu’o’i da azumi na kwana bakwai don ganin an yi zabe cikin kwanciyar ankali da gaskiya a jihar.

Mista Charles Egumgbe, Darakta Janar na kungiyar kamfen din Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya sanar da hakan a ranar Alhamis a Enugu yayinda yeke zantawa da manema labarai kan ayyukansu.

Egumgbe ya bayyana cewa azumin da addu’o’in zai fara daga 1 ga watan Disamba zuwa 7 ga watan Disamba.

2019: PDP ta kaddamar da addu’o’i da azumin kwana 7 don yin zabe cikin zaman lafiya a Enugu

2019: PDP ta kaddamar da addu’o’i da azumin kwana 7 don yin zabe cikin zaman lafiya a Enugu
Source: Depositphotos

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa kamfen din gwamna da yan majalisun jiha zai fara a ranar a ranar 1 ga watan Disamba a fadin kasar.

Darakta janar din ya bayyana cewa za su yi hakan ne kamar yadda yake a tsarin gwamnatin Ugwuanyi.

KU KARANTA KUMA: Bacewar biliyoyin naira: Majalisar dattawa za ta bincike hukumar kula da tashoshin ruwa

Ya bayyana cewar gwamnan na da imani ga Allah kuma zai so ya nemi yardar mai dukka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel