Gwamnatin Buhari ta sankame asusun bankunan wadanda suka yi badakala da dukiyar kasa

Gwamnatin Buhari ta sankame asusun bankunan wadanda suka yi badakala da dukiyar kasa

- Gwamnatin tarayya ta sanya takunkumi ga asusun bankunan duk wadanda hukumar INEC ta shigar da kara kansu a kotu bisa zargin cin hanci da rashawa

- Wannan na daga cikin aiwatar da dokar shugaban kasa ta 6 (Executive Order No. 6) kan "adana kadarorin da suke da alaka da zargin cin hanci da rashawa da dangogi"

- A ranar Talata, Olisa Metuh, tsohon kakakin jam'iyyar PDP, ya ce a yanzu bashi da kudin da zai ciyar da iyalansa, kasancewar EFCC ta sawa asusun bankinsa takunkumi

Gwamnatin tarayya ta sanya takunkumi ga asusun bankunan duk wadanda hukumar da ke yaki da masu yiwa dukiyar jama'a zagon kasa INEC ta shigar da kara kansu a kotu bisa zargin cin hanci da rashawa.

Bisa rahotannin da Legit.ng ta samu daga TheCable, wannan na daga cikin aiwatar da dokar shugaban kasa ta 6 (Executive Order No. 6) kan "adana kadarorin da suke da alaka da zargin cin hanci da rashawa da dangogi" wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a watan Oktoba, 2018.

Gwamnatin tarayya ta kuma sanya takunkumin fita wasu kasashe ga duk wadanda ake tuhuma, sai dai har yanzu ba a sanar da sunayen wadanda aka sanya masu takunkumin ba.

KARANTA WANNAN: EFCC: Kotun daukaka kara ta garkame shugaban hukumar SUBEB shekaru 41 a gidan kaso

Gwamnatin Buhari ta sankame asusun bankunan wadanda suka yi badakala da dukiyar kasa

Gwamnatin Buhari ta sankame asusun bankunan wadanda suka yi badakala da dukiyar kasa
Source: UGC

"Na baiwa wani abokina chekin N250,000, amma an dawo mun da shi," a cewar tsohon minista wanda dokar ta shafa.

"A lokacin da na kira jami'in da ke kula da asusuna, sai ya kirani don mu tattauna, a inda ya sanar da ni cewa dokar da shugaban kasar ya sawa hannu ta sa takunkumi ga asusuna dana wasu mutane. Duk wadanda ake tuhuma a kotu dokar ta shafe su" a cewarsa.

A ranar Talata, Olisa Metuh, tsohon kakakin jam'iyyar PDP, ya ce a yanzu bashi da kudin da zai sai koda magani ne, balle ayi maganar ciyar da iyalansa, kasancewar EFCC ta sawa asusun bankinsa takunkumi.

A ranar 30 ga watan Maris, Ministan watsa labarai, Lai Mohammed, ya saki sunayen wadanda ake tuhuma da cin hanci da rashawa, biyo bayan kalubalantarsa da Kola Ologbondiyan yayi, mai magana da yawun jam'iyyar PDP.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel