Ana sa ran cutar Kanjamau za ta kassara Matasa 360,000 zuwa shekarar 2030 - UNICEF

Ana sa ran cutar Kanjamau za ta kassara Matasa 360,000 zuwa shekarar 2030 - UNICEF

- Wata Cuta na yiwa Matasa 360, 000 barazanar Mutuwa daga yanzu zuwa shekarar 2030 - UNICEF

- Akwai yiwuwar Cutar Kanjamau za ta kassara rayuka Matasa 360, 000 a duniya

- Rashin kulawa da Cutar Kanjamau na barazana ga Mutuwar Yawa a tsakanin Matasan Duniya

Wani sabon rahoto da majalisar dinkin duniya reshen kulawa da yara watau UNICEF ta fitar a yau Alhamis ya bayyana cewa, rashin bayar kulawa mai muhimmanci ga cutar kanjamau na barazana ga salwantar rayukan Matasa 360, 000 a duniya daga yanzu zuwa shekarar 2030.

Alkalumma a halin yanzu sun tabbatar da cewa, tuni an yi nisa daga kan turba ta manufar tsarkake duniya wajen kawo karshen cutar kanjamau a tsakanin Yara zuwa shekarar 2030 kamar yadda shugaban cibiyar UNICEF, Henrieeta Fore ta bayyana.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, binciken ya tabbatar da cewa, za a samu rangwami na adadin kananan Yara masu dauke da cutar kanjamau da kuma rangwami na salwantar rayukan yaran da ke kasa da shekaru 14 a duniya.

Shugabar UNICEF; Henrieeta Fore

Shugabar UNICEF; Henrieeta Fore
Source: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan kididdiga ta tabbatar da yadda cutar kanjamau ke barazanar salwantar rayukan Matasa 360, 000 da ke tsakanin shekarun haihuwa na 15 zuwa 19 daga yanzu zuwa shekarar 2030.

KARANTA KUMA: Gwamnati na ta taka rawar gani ta dakusar da ta'addanci Boko Haram a jihar Borno - Buhari

Binciken ya tabbatar cewa, ci gaba da ta'azzarar wannan annoba ta cutar kanjamau na da nasaba ne da rashin kulawa da kuma rashin tsarkake kai da ababen da ke haddasa yaduwar cutar a tsakankanin al'umma.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yayin da ake ci gaba da fama da cutar Ebola da ta kassara rayukan mutane kimanin 200, cutar zazzabin cizon sauro ta kuma barke a jamhuriyyar kasar Congo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel