An cire Texas Chukwu, an mayar da Sani Kukasheka matsayin kakakin hukumar Sojin Najeriya

An cire Texas Chukwu, an mayar da Sani Kukasheka matsayin kakakin hukumar Sojin Najeriya

Hukumar sojin Najeriya ta cire Janar Texas Chukwu matsayin kakakinta, Jaridar The Cable ta bada rahoto.

Wata majiyar hukumar ta bayyana cewa an cire Texas Chukwu ne bayan koke-koke daga wurare daban-daban bisa ga rashin kwarewarsa wajen yada labaran yaki da ta’addanci da hukumar keyi.

Majiyar tace: “Chukwu bai iya manajin kafofin yada labarai kuma ya gaza dabbaka ayyukan da ya samu a kasa,”

“Kakakin hukuma mai kokarin ya kamata ya rika Magana da abubuwan da suka shafi hukumar a lokaci bayan lokaci da kuma samar da mafita. Gazawarsa ya maishe da hukumar sojin Najeriya abin dariya a idon duniya.”

Saboda haka, an nada tsohon Kakakin, Birgeidya Janar Sani Usman Kukasheka.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon ziyarar Buhari Maiduguri

Chukwu ya zama kakakin hukumar ne a watan Fabrairun da ya gabata ne yayinda Kukasheka ta tafi makarantan ilimin strateji a Kuru, garin Jos.

Yayinda aka tuntubi, Janar Sani Usman Kukasheka, ya tabbatar da wannan labara kuma yace ya koma tsohon mukaminsa ranan Litinin.

Kamar yadda aka lura, Kukasheka ne ya yi aikin mai jagoran taro a jiya Laraba a Maiduguri da shugaba Muhammadu Buhari ya halarta.

Hukumar sojin Najeriya ta sha suka iri-iri a kwanakin bayan nan musamman bayan harin kwantan baunar da yan kungiyar Boko Haram suka kaiwa jami’an soji a Matele.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel