Yanzu Yanzu: Dan takarar Amosun da wasu mambobbin majalisar wakilai 3 sun sauya sheka

Yanzu Yanzu: Dan takarar Amosun da wasu mambobbin majalisar wakilai 3 sun sauya sheka

Rahotanni da ke zuwa mana ya nuna cewa Adekunle Akinlade, dan takarar gwamna da gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya fi so, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar Allied People’s Movement (APM).

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Akinlade, wanda ya fadi zaben fidda gwani na takarar gwamna karkashin jam’iyyar APC a jihar ya bar jam’iyyar ne tare da wasu mambobi uku.

Sauran wadanda suka sauya shekar sune Kaugama (Jigawa) wanda ya bar jam’iyyar PD zuwa Social Democratic Party (SDP), Mohammed Ajanah (Kogi) daga APC zuwa PDPsai kuma Salisu Koko (Kebbi) daga APC zuwa SDP.

Yanzu Yanzu: Dan takarar Amosun da wasu mambobbin majalisar wakilai 3 sun sauya sheka

Yanzu Yanzu: Dan takarar Amosun da wasu mambobbin majalisar wakilai 3 sun sauya sheka
Source: Twitter

A halin da ake ciki, Mukaddashin shugaban hukumar yaki da ci hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu ya ce hukumar za ta kula da kudaden gudunmawa fa jam’iyyun siyasa a zaben 2019 da kuma gudunmawar mutane daban-daban.

Magu ya bayyana haka a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba yayinda yake gabatar da wata takarda a taron kwana daya na gwamnonin jihohi 36 da masu ruwa da tsaki.

KU KARANTA KUMA: Goyon bayan Buhari bai haddasa gaba a tsakanina da mahaifina ba – Dan Obasanjo

Da ya samu wakilcin Olanipekun Olukoyede, shugaban aikatansa, shugaban EFCC din ya ce hukumar ba za ta bari a karkatar da kudin jama’a zuwa kudin kamfen ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel