EFCC: Kotun daukaka kara ta garkame shugaban hukumar SUBEB shekaru 41 a gidan kaso

EFCC: Kotun daukaka kara ta garkame shugaban hukumar SUBEB shekaru 41 a gidan kaso

- Kotun daukaka kara da ke zama a Sokoto, ta yankewa shugaban hukumar SUBEB na jihar Zamfara, Murtala Adamu Jengebe, hukuncin shekaru 41 a gidan kaso

- Kotun ta yankewa Jengebe wannan hukuncin ne baya da ta same shi dumu dumu da aikata laifuka 7 cikin goma da hukumar EFCC ta ke zarginsa da aikatawa

- Haka zalika, kotun ta bayar da umurni cewa zai yi zaman wakafin ne na shekaru 41 kai tsaye (a lokaci daya)

Wani kwamitin bincike na mutane biyar da kotun daukaka kara da ke zama a jihar Sokoto ta kafa karkashin mai shari'a Hannatu Sankey, ta yankewa shugaban hukumar ilimi bai daya ta jiha (SUBEB) na jihar Zamfara, Murtala Adamu Jengebe, hukuncin shekaru 41 a gidan kaso.

Kotun ta yankewa Jengebe wannan hukuncin ne baya da ta same shi dumu dumu da aikata laifuka 7 cikin goma da ake zarginsa da shi a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zama a Gusau, jihar Zamfara.

Kotun daukaka karar, ta bayyana cewa wanda ake zargin, an same shi da aikata laifuka 7 cikin goma, da suka shafi tu'annadi da dukiyar jama'a, wanda hukumar EFCC ta shigar akansa. An yanke masa shekaru 20 a kan laifuka 4, sai kuma shekaru 21 akan laifuka 3.

KARANTA WANNAN: Surukina zai tsaya takarar gwamnan jihar Imo karkashin wata jam'iyya ba APC ba - Okorocha

EFCC: Kotun daukaka kara ta garkame shugaban hukumar SUBEB shekaru 41 a gidan kaso

EFCC: Kotun daukaka kara ta garkame shugaban hukumar SUBEB shekaru 41 a gidan kaso
Source: Depositphotos

Haka zalika, kotun ta bayar da umurni cewa zai yi zaman wakafin ne na shekaru 41 kai tsaye (a lokaci daya).

Idan za a iya tunawa, a ranar 12 ga watan Mayu 2017, babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zama a Gusau, karkashin jagorancin mai shari'a Z.B Abubakar ta watsar da zargin aikata laifuka 10 da ake yiwa shugaban hukumar ta SUBES na tu'annadi da dukiyar jama'a, sai dai ta same shi da laifin yin aiki a wani kamfani mai zaman kansa, a hannu daya kuma yana aikin gwamnati. Laifin da hukumar bata shigar da kara kansa ba.

Rashin gamsuwa da wannan hukunci na mai shari'a Z.B Abubakar, mai shigar da karar, (hukumar EFCC) ta garzaya kotun daukaka kara da ke zama a Sokoto, don ganin cewa an bi diddigin shari'ar tare da yin watsi da hukuncin da babbar kotun gwamnatin tarayyar ta yanke.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel