Za mu zuba idanu akan kudaden kamfen din zaben 2019 - EFCC

Za mu zuba idanu akan kudaden kamfen din zaben 2019 - EFCC

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da ci hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu ya ce hukumar za ta kula da kudaden gudunmawa fa jam’iyyun siyasa a zaben 2019 da kuma gudunmawar mutane daban-daban.

Magu ya bayyana haka a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba yayinda yake gabatar da wata takarda a taron kwana daya na gwamnonin jihohi 36 da masu ruwa da tsaki.

Da ya samu wakilcin Olanipekun Olukoyede, shugaban aikatansa, shugaban EFCC din ya ce hukumar ba za ta bari a karkatar da kudin jama’a zuwa kudin kamfen ba.

Za mu zuba idanu akan kudaden kamfen din zaben 2019 - EFCC

Za mu zuba idanu akan kudaden kamfen din zaben 2019 - EFCC
Source: Depositphotos

Ya ce ana bukatar yan siyasa su rubuta dukkanin gadunmawar da suka karba da kuma sunayen wadanda suka bayar da tallafi da kyau sannan su shirya nuna hakan ga hukumomin tsaro a karshen zabe.

KU KARANTA KUMA: Fusatattun mutane a Kano sun yi wa ma’aikatan KEDCO dukan tsiya

Magu ya ce a duk lokacin da gwamnati ta karkatar da kudade do kamfen din wani zabe, sai ka ga kudade ne da aka danne na lafiya, tsaro, ilimi, ginin hanya, da sauran ayyukan cin gaban jama’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel