Laifi da hukunci: Shin mai aiki da ya kashe ogansa ya mutu ne ko yana raye?

Laifi da hukunci: Shin mai aiki da ya kashe ogansa ya mutu ne ko yana raye?

- Sunday Adefonuo Anani, da ake zargi da kashe Opeyemi Badamosi ya mutu a tsare

-An kama shi da laifin kashe shi da akayi har cikin gidanshi

- Kotun majistare dake Igbosere ce ta bada damar tsare shi a gidan kaso

Laifi da hukunci: Shin mai aiki da ya kashe ogansa ya mutu ne ko yana raye?

Laifi da hukunci: Shin mai aiki da ya kashe ogansa ya mutu ne ko yana raye?
Source: Depositphotos

Sunday Adefonuo Anani mai shekaru 22 a duniya da ake zargi da kashe Opeyemi Badamosi, shugaban Credit Switch Technology, ya mutu a gidan kaso.

An zargi Anani da laifin kisa a ranar 31 ga watan Octoba a gidan Badamosi dake lamba 3b layin Onikoyi dake Ikoyi a Legas.

Majiyar mu ta ruwaito cewa mai rasuwar yana tsare ne a gidan kaso wanda kotun majistare dake Igbosere a jihar Legas ta bukaci hakan.

DUBA WANNAN: Duniya tayi Allah-wadai da Saudiya bayan da ta dawo da littafan zafafa ra'ayi a makarantun ta

A ranar 12 ga watan Nuwamba ne kotun ta dage sauraron kara zuwa 18 ga watan Disamba kafin isowar shawarar shari'a daga DPP.

Majiyar mu ta samo cewa lauyan dake kare Anani ya samu sakon mutuwar ta ne a ranar 28 ga watan Nuwamba cewa ta rasu a gidan yarin. Bayani akan mutuwar dai har yanzu bai samu ba.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel