‘Yar shekara 3 ta mutu bayan da wani makwabcin su ya yi mata fyade a Zaria

‘Yar shekara 3 ta mutu bayan da wani makwabcin su ya yi mata fyade a Zaria

Wata babbar kotu da ke zaune a garin Zariya na jihar Kaduna ta yankewa wani mutum mai suna Shehu Usman Bashir hukuncin zama a gidan wakafi akan zargin yiwa yarinya ‘yar shekara 3 fyade har sai da ta mutu.

Maishari’a Kabir Dabo ne ya bayar da umurnin a zaman kotu, bayan da ya yi watsi da bukatar wanda ake zargin na neman beli.

Ana dai zargin Shehu ne da laifukka biyu wadanda suka hada da fyade da kuma kisan kai.

‘Yar shekara 3 ta mutu bayan da wani makwabcin su ya yi mata fyade a Zaria

‘Yar shekara 3 ta mutu bayan da wani makwabcin su ya yi mata fyade a Zaria
Source: Depositphotos

Tun da farko, mai gabatar da kara na gwamnatin jihar Kaduna, Hajiya Jummai Adamu-Dan’azumi, ta bayyana wa kotun cewa, wanda ake tuhumar na fuskantar zargi biyu ne da suka hada da fyade da kuma kisan kai wanda dukkansu laifi ne a karkashin sashe na 221 na dokar Fane Kot.

Ta ce, wanda ake zargin na zama ne a Yan Bita, dake unguwan Liman, a Sabon Garin Zariya, ta jihar Kaduna, yana kuma makwabaka ne da iyayen yarinyar da ya yiwa fyaden Bayani ya nuna cewa, mutumin ya yaudari yarinyar ne zuwa dakinsa inda ya yi mata fyade har ta mutu.

KU KARANTA KUMA: 2019: Jam’iyyun siyasa za su kulla yarjejeniyar zaman lafiya

Lauyar ta gwamnatin ta kara da cewa, bayan da ba a ga yarinyar bane aka shiga neman a makwabta, daga baya ne aka nemi lallai sai an binciki dakin wanda ake zargin, a nan ne, bayan da aka binciki dakin a ka ga gawar yarinyar kunshe a cikin wani tsuma a mace.

Alkalin Kotun dai ya daga sauraron karar zuwa ranar 15 na watan Disamba don ci gaba da karbar shaidu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel