An fasa kwai: Babban dalilin da yasa likitocin Najeriya suke hijira zuwa kasashen waje

An fasa kwai: Babban dalilin da yasa likitocin Najeriya suke hijira zuwa kasashen waje

Kungiyar likitocin Najeriya, ta kasa, NMA, ta bayyana babban dalilin da yasa likitoci yan Najeriya basa zama, suka gwammace su fita zuwa kasashen waje, musamman kasashen Turai, na Larabawa da kuma Amurka don yin aikinsu.

Majiyar Legit.com ta ruwaito shugaban kugiyar NMA reshen babban birnin tarayya Abuja, Dakta Ekpe Phillips ne ya bayyana haka a yayin taron ranar kiwon lafiya ta kungiyar kananan likitoci da aka yi a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Zaben 2019: Abadulsalam Abubakar ya bayyana jihohin 6 da za’a iya samun rikici

A jawabinsa, Dakta Ekpe yace rashin kayan aiki da karancin albashi ne yasa likitocin Najeriya basa zama su yi aiki a asibitocin kasar, don haka suka gwammace su fita zuwa inda zasu samu albashi mai tsoka, tare da samun isassun kayan aiki don yin aiki cikin natsuwa.

A cewar Ekpe, albashin likitoci a Najeriya ba wani abin kirki bane, don haka yayi kira ga gwamnati da ta yi ma likitoci karin albashi don magance matsalar, haka zalika yace dayawa daaga cikin likitocin da suka yi hijira zuwa kasashen waje sun fita ne saboda rashin kayan aiki anan.

Bugu da kari ya kara da cewa a yanzu haka ana samun karancin guraben aiki ga likitoci a Najeriya, sa’annan akwai karancin guraben horas da matsakaitan likitoci a cibiyoyin kiwon lafiya dake Najeriya, kuma yace wannan ma na taimaka ma wajen tunzura likitoci su fita su bar Najeriya.

“Muna samun rahotannin cewa Likitoci sun yanke jiki sun fadi, ba komai bane illa tarin aikin dake kanmu, hakan kuma ya faru ne saboda abokan aikinmu sun bar Najeriya, don haka aikinmu ya karu. A yanzu haka likita daya yana duba marasa lafiya dubu biyar, a maimakon mutum 600.

“Abin haushinma shine gwamnati bata damu ba, ko a jikinta, don kuwa ba ta ma kula ba, balle kuma a fara lalubar bakin zaren, ta yadda za’a sa ran iya maganceta.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel