Goyon bayan Buhari bai haddasa gaba a tsakanina da mahaifina ba – Dan Obasanjo

Goyon bayan Buhari bai haddasa gaba a tsakanina da mahaifina ba – Dan Obasanjo

Dan tsohon shugaban kasa Olusegun wanda keg yon bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019, Olujonwo Obasanjo ya ce shawarar da ya dauka na marawa shugaban kasar baya bai haddasa ko wani gaba a tsakaninsa da mahaifinsa ba.

A cewarsa yana goyo bayan shugaba Buhari ne saboda duba da yake yi ga makomar matasan Najeriya a nan gaba.

Obasanjo karmi wanda yayi Magana a wani taron manema labarai da APC Press Corp ta shirya ya ce duk da goyon bayan yan takarar shugaban kasa daban-daban da suke yi, bbabu abunda ya canja a iyalan Obasanjo ta fannin hadin kai da soyayya.

Goyon bayan Buhari bai haddasa gaba a tsakanina da mahaifina ba – Dan Obasanjo

Goyon bayan Buhari bai haddasa gaba a tsakanina da mahaifina ba – Dan Obasanjo
Source: Facebook

Sannan ya kara da cewar goyon bayan dan takara daban ba yana nufin ya bar ahlinsa bane.

KU KARANTA KUMA: 2019: Jam’iyyun siyasa za su kulla yarjejeniyar zaman lafiya

Ya kuma kara da cewa babu adalci ga duk mutumin da ya hada gwamnatin Buhari da wanda mahaifinsa ya jagoranta cewa dukkanin gwamnatocin biyu sun hau mulki a lokaci mabanbanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel