Surukina zai tsaya takarar gwamnan jihar Imo karkashin wata jam'iyya ba APC ba - Okorocha

Surukina zai tsaya takarar gwamnan jihar Imo karkashin wata jam'iyya ba APC ba - Okorocha

- Gwamna Rochas Okoracha, ya bada haske kan cewar surukinsa, Uche Nwosu, zai yi takarar kujerar gwamnan jihar Imo a karkashin wata jam'iyyar ba APC ba

- Okorocha ya ce ba zai hana duk wanda yake ganin APC bata yi masa dai-dai ba ficewa daga jam'iyyar

- Akalla mambobin majalisar dokoki da na tarayya 27 daga jihar Imo, da suka hada da Nwasou ne ake ganin cewa za su iya ficewa daga jam'iyar APC kafin ranar 1 ga watan Disamba

A jiya ne Gwamna Rochas Okoracha, ya bada haske kan cewar surukinsa, wanda kuma shine tsohon shugaban ma'aikatansa, Uche Nwosu, zai yi takarar kujerar gwamnan jihar Imo a karkashin wata jam'iyyar ba APC ba.

Nwosu, wanda yana daya daga cikin wadanda suka tsaya takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC, dama sauran wadanda basu samu nasara a zaben fitar da gwani ba, na iya barin jam'iyyar APC zuwa wasu jam'iyyu don cika muradunsu na siyasa.

Okorocha ya ce ba zai hana duk wanda yake ganin APC bata yi masa dai-dai ba ficewa daga jam'iyyar.

KARANTA WANNAN: Masha Allah: An rantsar da sabbin lauyoyi 4,779 a Nigeria

Surukina zai tsaya takarar gwamnan jihar Imo karkashin wata jam'iyya ba APC ba - Okorocha

Surukina zai tsaya takarar gwamnan jihar Imo karkashin wata jam'iyya ba APC ba - Okorocha
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattara bayanai kan cewa akalla mambobin majalisar dokoki na jihar Imo da kuma 'yan majalisun tarayya 27, da suka hada da Nwasou ne suke ganin cewa jam'iyar APC bata yi masu adalci a zabukanta na fitar da gwani ba, kuma suna shirin ficewa daga jam'iyyar zuwa wasu jam'iyyu kafin rufe kofar sauya 'yan takara a ranar 1 ga watan Disamba.

Okorocha ya bayyana cewa zai kasance mai goyon bayan takararus a kowacce jam'iyya suka koma, amma shi zai tsaya takarar kujerar sanata mai wakiltar mazabar Orlu a majalisar dattawa.

Sai dai gwamnan, ya kara jaddada cewa, Nwosu da sauran 'yan takarar da aka yiwa ba dai-dai ba, sune zabinsa a kowacce jam'iyya suka koma.

Haka zaika gwamnan jihar Imon ya tabbatarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewar magoya bayansa zasu tsaya kai da fata don tabbatar da tazarcensa tare da shan alwashin daukar mataki aka duk wanda ya bijire masa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel