Zaben 2019: Abadulsalam Abubakar ya bayyana jihohin 6 da za’a iya samun rikici

Zaben 2019: Abadulsalam Abubakar ya bayyana jihohin 6 da za’a iya samun rikici

Kwamitin zaman lafiya ta kasa dake karkashin shugabancin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Abdulsalam Abubakar ya bayyana fargabarsa game da yiwuwar samun tashin tashina a wasu jihohin Najeriya a yayin zaben 2019.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Abdulsalam ya bayyana haka ne bayan gaanwar kwamitin da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Mahmoud Yakub a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba 28 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Kungiyoyin Musulmai sun nemi a nada Inyamiri babban limamin Masallacin Abuja

Tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar ya bayyana jahar Ribas, da jihohin yankin Arewa maso gabas da suka hada da jahar Gombe, Yobe, Borno, Yobe da Adamawa daga cikin jihohin da yake tsoron barekewar rikicin a cikinsu a zaben 2019.

Sai dai Abdulsalam yace kwamitin zaman lafiya ba zata gajiya ba, zasu cigaba da wayar da kawunan jama’a, tare da ganawa da shuwagabannin jam’iyyu da sakatarorinsu don jan hakulansu game da muhimman gudanar da zaben gaskiya da gaskiya da kuma zaman lafiya.

“Akwai matsala a jahar Ribas, kuma akwai wasu yankunan da ake samun sabbin matsaloli, don haka zamu yi iya bakin kokarinmu don ganin mun shawo kan matsalar. Ina damuwa game da matsalar tsaro da muke fama da ita a yankin Arewa maso gabas.

“Kuma ya zama wajibi mu kawo karshen matsalar domin a baiwa hukumar INEC daman shirya zabe sahihi a fadin jihohin dake yankunan, domin kuwa INEC ba zata tura jami’anta su yi aikin zabe cikin hadari ba, don haka ina fatan zamu shawo kan matsalar kafin lokacin zabe.” Inji shi.

A nata bangaren, hukumar INEC ta baiwa kwamitin tabbacin a shirye take ta gudanar da zaben gaskiya da gaskiya ba tare da magudi, aringizo ko rinton kuri’u ba, kamar yadda shugabanta Farfesa Yakubu ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel