Hukumar LASTMA ta yi magana kan jami’inta da jami’in SARS ya hallaka

Hukumar LASTMA ta yi magana kan jami’inta da jami’in SARS ya hallaka

Hukumar lura da rage cinkoso hanyoyin jihar Legas LASTMA ta tabbatar da kisan daya daga cikin jami’anta mai suna Adeyemo Rotimi, wanda aka kasha a jiya Laraba, 28 ga watan Nuwamba.

Ta bayyana hakan ne a jawabin da ta saki da safen nan ta shafin ra’ayi da sada zumuntarta na Tuwita.

A cewar hukumar: “Muna matukar bakin cikin tabbatar da kisan daya daga cikin jaruman ma’aikatanmu, Adeyemo Rotimi, wanda wani jami’an hukumar SARS ya hallaka yayinda yake gudanar da aikinsa a Iyana Ipaja.”

Hukumar LASTMA ta yi magana kan jami’inta da jami’in SARS ya hallaka

Hukumar LASTMA ta yi magana kan jami’inta da jami’in SARS ya hallaka
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Buhari ya tafi kasar Chadi kan rikicin Boko Haram

Mun kawo muku rahoton cewa wani da ake zargin jami’in ya sanda masu yaki da yan ta’adda ne (SARS) ya hari wani jami’in kula da cunkoso a titi na jihar Lagas wato State Traffic Management Authority (LASTMA) har lahira.

A cewar jaridar The Nation, lamarin ya afku ne a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba a shataletalen Iana-Ipaja da misalin karfe 6 na yamma.

Jami’in LASTMA din ya tsayar da shi kan lamarin zirga-zirgan motoci.

Legit.ng ta tattaro cewa sai jami’in ya sauka sannan ya gargadi jami’in da ke kula zirga-zirgn motocin kan cewa kada ya sake tayar da shi, inda ya kara da cewa bashi da yancin yin haka.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel