2019: Jam’iyyun siyasa za su kulla yarjejeniyar zaman lafiya

2019: Jam’iyyun siyasa za su kulla yarjejeniyar zaman lafiya

Shugaban kwamtn zaman lafiya na kasa, Janar Abdulsalam Abubakar, ya bayyana cewa dukkanin shugabannin jamiyyun siyasa za su kulla yarjejeniyar zaman lafiya don zaben 2019.

A cewersa, kulla yarjejenyar zai taimaka wajen taka gagarumar rawar gani akan nasarar zabe mai zuwa.

Abubakar ya bayyana hakan a lokacin wata ganawa da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Mahmoud Yakubu a Abuja a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba.

2019: Jam’iyyun siyasa za su kulla yarjejeniyar zaman lafiya

2019: Jam’iyyun siyasa za su kulla yarjejeniyar zaman lafiya
Source: Twitter

Ya ce: “Za mu yi iya bakin kokarinmu wajen ganin lamarin siyasa ya tafi daidai.

“Ku ma mambobin kafofin watsa labarai kuna da naku rawar gwanin da za ku taka da kuma wayar da mutanenmu da yan siyasa kai saboda kada su yi kamfen din da zai haddasa tarzoma yayin kafen dinsu.

“Gobe za mu gana da dukkanin shugabanni da sakatarorin jam’iyyun siyasa da ke da rijista.

KU KARANTA KUMA: Buratai ya yi martani akan harin Matele, ya ce a bu rudunar sojin da za ta iya samun isasshen kayayyakin aiki

“Kudirin ganawar shine jam’iyyun siyasa za su kulla yarjejeniyar fahimta kan yadda za’a gudanar da kamfen ba tare da dacin rai ba."

A nashi bangaren shugaban INEC ya ba yan Najeriya tabbacin cewa za su tabbatar da zabe na gaskiya a 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel