Buratai ya yi martani akan harin Matele, ya ce a bu rudunar sojin da za ta iya samun isasshen kayayyakin aiki

Buratai ya yi martani akan harin Matele, ya ce a bu rudunar sojin da za ta iya samun isasshen kayayyakin aiki

Shugaban hafsan sojoji, Laftanal Janar Tukur Buratai ya ce babu rundunar sojin da za ta iya mallakar isasshen kayyakin yaki.

Buratai wanda yayi Magana akan harin Metele a lokacin taron ma’aikatan hukumar soji a Maiduguri a ranar Laraba, 28 ga watan Nuwamba ya ce rundunar sojoji ta shirin wasu dabaru don kawo karshen yan ta’addan Boko Haram a arewa maso gabas.

Buratai ya kuma bayyana shirye-shiryen zaben 2019, cewa rundunar sojin za ta gudanar da Operation Safe Conduct a kasar don tabatar da zabe na gaskiya.

Buratai ya yi martani akan harin Matele, ya ce a bu rudunar sojin da za ta iya samun isasshen kayayyakin aiki

Buratai ya yi martani akan harin Matele, ya ce a bu rudunar sojin da za ta iya samun isasshen kayayyakin aiki
Source: Depositphotos

Ya kara da cewa babu rundunar sojin da za ta iya mallakar isassun kayyaki don gudanar da ayyukanta. Don haka ya zama wajibi ga dukkanin kwamandoji su san cewa muna cikin wani jerin yaki da ke bukatar karfafawa da sauya launi.

Buratai ya kuma bukac sojoji da su kasance a tsaka-tsaki lokacin zabe.

A baya mun ji cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a matsayinsa na shugaban kasa da kuma karfin da yake da shi, zai tabbatar da cewa gwamnati ta samar da makaman yakin zamani domin kawar da haukan Boko Haram.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram na kai wa sojoji farmaki da jirage marasa matuka

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda yake jawabi a birnin Maiduguri, jihar Borno a yau Laraba, 28 ga watan Nuwamba yayinda ya tafi halartan taron babban hafsan sojin Najeriya da ke gudana a jihar.

Ya jajantawa hukumar sojin Najeriya bisa ga rashin akalla sojoji 44 da sukayi a makon da ya gabata sakamakon harin Boko Haram kan barikin Matele dake arewacin jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel