Abu biyu kacal gwamnatin Buhari ta samar - PDP

Abu biyu kacal gwamnatin Buhari ta samar - PDP

A wani jawabi da jam'iyyar PDP ta yi a jiya, Laraba, ta bakin kakakinta, Kola Ologbondiyan, ta ce babu wani abu da gwamnatin Buhari ta samar a Najeriya sai yunwa da tashin hankali.

Jam'iyyar PDP ta kara da cewar 'yan Najeriya na zasu kara zabar Buhari ba saboda danniya da wahalar da gwamnatinsa ta jefa su a ciki.

Kakakin na jam'iyyar PDP ya zargi shugaba Buhari da nuna da son kai, nuna halin ko-in-kula, gazawa, da kawo rabuwar kai tsakanin 'yan Najeriya.

Ologbondiyan na wadannan kalamai ne yayin karbar wasu dumbin matasa daga jihohin Kano, Katsina, da Kaduna yayin da su ka ziyarci ofishin PDP domin tabbatar da ficewar su daga jam'iyyar APC tare da jaddada goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar.

Abu biyu kacal gwamnatin Buhari ta samar - PDP

Kola Ologbondiyan
Source: Depositphotos

Ko a yammacin ranar Litinin sai da Legit.ng ta kawo ma kulabarin cewar kungiyar APC National Youth Vanguard karkashin shugabancin Alhaji Jibrilla Agama ta jagoranci wasu kungiyoyin matasa 60 zuwa jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Babbar magana: 'Yan sanda sun kama AIG na bogi a arewacin Najeriya

A sanarwar da kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, ya fitar a shafinsa na Tuwita ya ce kungiyoyin matasan sun koma PDP ne domin marawa dan takarar jam'iyyar, Atiku Abubakar, baya a zaben shekarar 2019.

A cewar sa, matasan sun ce APC ba jam'iyyar da ta dace da matasan Najeriya ba ce.

An karbi matasan ne a hedkwatar jam'iyya PDP dake Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel